'Yan wasan Bundesliga a gasar cin kofin Afrika
Gasar Bundesliga ta rasa wasu muhimman 'yan kwallo sakamakon halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a kasar Kamaru. AFCON da ta kunshi kasashe 24 na gudana ne daga 9 ga watan Janairu zuwa 7 ga Fabrairun 2022.
Bayern Munich – Eric Maxim Choupo-Moting da Bouna Sarr
Bayern Munich da ke saman teburin Bundesliga na wasa ba tare da Eric Maxim Choupo-Moting (hoto) da Bouna Sarr ba sakamakon gasar AFCON. Suna buga wa biyu daga cikin kasashen da ake ji da su na tsawon makonni hudu. Kamaru mai masaukin baki ta lashe gasar sau biyar kuma tana fatan lashe gasar a karon farko a gida tare da taimakon Choupo-Moting. Ita kuwa Senegal tana neman kofin farko tare da Sarr.
Bayer Leverkusen – Odilon Kossounou da Edmond Tapsoba
Leverkusen ta yi rashin 'yan wasan baya Odilon Kossounou (hoto) na Côte d'Ivoire da Edmond Tapsoba na Burkina Faso. Kossounou ya zama babban dan wasa na Les Elephants tun bayan da ya fara taka leda a shekarar 2020. Suna da burin lashe kofin Afirka na uku, yayin da Burkina Faso ke neman na farko.
Hoffenheim – Diadie Samassékou
Dan wasan Hoffenheim daya ne a gasar cin kofin Afrika, Diadie Samassekou na Mali. Najeriya ba ta kira dan wasan baya Kevin Akpoguma, tsohon kyaftin din Jamus na 'yan kasa da shekara 20 bayan da ya fara taka leda a shekarar 2020 ba. Shi ma Kasim Adams Nuhu, kasarsa ta Ghana ba ta dama da shi ba.
RB Leipzig – Amadou Haidara da Ilaix Moriba
Red Bulls ta samu wakilcin ‘yan wasan tsakiya Amadou Haidara (hoto) na Mali da Ilaix Moriba na Guinea a gasar AFCON. Haidara ya fara buga wasansa na farko a matsayin sana'a a shekara ta 2017, kuma zai taimaka wajen kai Mali ta yammacin Afirka zuwa wasan karshe a birnin Yaounde a ranar 7 ga Fabrairu. Shi kuwa Moriba kwanan nan ya yi mubaya'arsa daga Spain zuwa Guinea, inda aka haife shi.
Union Berlin – Taiwo Awoniyi
Union Berlin ta yi rashin dan wasan da ya fi zura kwallo a raga Taiwo Awoniyi (hoton sama, a dama) don halartar gasar cin kofin Afrika, inda zai buga wa Najeriya da ta lashe kofin gasar sau uku. Kasancewa yana da kwallaye tara a wasanni 17 na Bundesliga kafin hutun lokacin sanyin hunturu, kungiyarsa za ta yi kewar Awoniyi sosai.
Cologne – Ellyes Skhiri
Skhiri ya dawo ne daga wasan kasa da kasa na karshe da ya yi a watan Oktoba da rauni, wanda ya hana shi buga wa Cologne wasa har zuwa lokacin hutun sanyin hunturu. Amma ya yunkuro yanzu a matsayin babban jigo a tawagar Tunisiya, wacce ke neman kara lashe gasar bayan kofin AFCON daya tilo da ta samu a 2004.
Eintracht Frankfurt – Aymen Barkok
Ga dan wasan da ya yi fama da matsala a Eintracht Frankfurt, gasar cin kofin kasashen Afirka ba za ta zo a mafi kyawun lokaci ba. Aymen Barkok na cikin tawagar Maroko da ke fatan lashe kofin karo na biyu bayan na 1976. Shi haifaffen Frankfurt din da ya rasa tagomashinsa a kungiyar Eintracht Frankfurt, yana iya neman samun nasara a kan 'yan wasa a Kamaru.
Borussia Mönchengladbach – Ramy Bensebaini
Ramy Bensebaini na Mönchengladbach ya je Kamaru ne domin ya taimaka wajen kare kofin nahiyar Afirka da Aljeriya take rike da shi. Zakaran Afirka daya tilo a gasar Bundesliga, Bensebaini ya buga wasanni shida daga cikin bakwai na kungiyar Fennec lokacin da suka lashe gasar a 2019 a birnin Alkahira.
VfB Stuttgart – Omar Marmoush
Omar Marmoush dai ya fara buga wasansa na farko a Masar a shekarar 2021, amma tuni ya samu kansa a tawagar koci Carlos Queiroz yayin da "Fir'aunawan" Masar ke fafutukar ganin sun lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na takwas. Stuttgart za ta yi wasa ba tare da dan kwallon aron na tsawon makwanni hudu ba, idan suka kai wasan karshe a ranar 7 ga Fabrairu.
Paderborn – Jamilu Collins
Dan wasan baya na lig na biyu na Bundesliga zai kasance cikin tawagar Najeriya a gasar. Wannan ne karo na biyu da Collins zai fito a gasar ta AFCON bayan ya kammala a matsayi na uku da Super Eagles a shekara ta 2019.
St. Pauli – Daniel Kofi Kyereh
An fara kiran Daniel Kofi Kyere zuwa tawagar kasar Ghana a watan Satumban 2021 domin buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da kasar Habasha. Zai zama babban rashi ga kungiyar St. Pauli da ke Bundesliga na biyu, wacce ke neman hayewa zuwa babban rukuni na Bundesliga. Ya zura kwallaye biyar da taimakawa sau tara kafin Bundesliga 2 ya fara hutun lokacin sanyin hunturu.