1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Y'an tawayen Yemen sun harba rokoki kan Saudiyya

Suleiman Babayo
June 11, 2019

Sojojin Saudiyya sun bayyana kakkabo rokokin da 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka harba cikin kasar ta Saudiyya.

https://p.dw.com/p/3KC1y
DW Exclusive Deutsche Waffen in Jemen SPERRFRIST 26.02.2019 20 Uhr saudische Soldaten an der Grenze zu Jemen
Hoto: Imago/Kyodo News


'Yan tawayen kungiyar Houthi na kasar Yemen a wannan Talata sun bayyana kaddamar da hare-haren makamai rokoki guda biyu zuwa cikin kudu maso yammacin kasar Saudiyya. Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ruwaito wani jami'in soja ya tabbatar da kakkabo makaman rokokin guda biyu a wajen garin Khamis Mushait. 

'Yan tawayen na Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran, suna kara kaimi wajen kai farmaki kan kasar Saudiyya wadda take jagorancin kawancen da ke goyon bayan gwamnatin Yemen mai gudun hijira da kasashen duniya suka amince da ita.

Yakin basasan ya janyo mutuwar dubban fararen hula, yayin da wasu milyoyi ke fuskantar karancin abinci da magunguna gami da fari da ya tsagaiyara kasar ta Yemen wadda ke sahun gaba cikin kasdashe 'yan rabbana ka wadata mu.