'Yan Shi'a na shirin sulhu da gwamnatin Najeriya
October 19, 2019Talla
Kungiyar mabiya Shi'a a Najeriya ta ce tana shirye da ta zauna da gwamnatin kasar don sasantawa a wani yunkuri na samun zaman lafya tsakaninta da gwamnati.
Shugaban kungiyar na riko a kasar Shekh Yakubu Yahaya Katsina ne ya bayyana haka ga manema labaru a Katsina. inda ya ce kuniyar ta shirya duk wata tattaunawa da gwamnati ba tare da wani sharadi ba muddin gwamnatin ta Najeriya na bukatar hakan.