1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun kama jagoran adawa a Rasha

Yusuf Bala Nayaya
May 5, 2018

Jagoran adawa a Rasha Alexei Navalny an kama shi a wannan rana ta Asabar bayan fita zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Vladimir Putin a birnin Moscow.

https://p.dw.com/p/2xEJI
Anti-Putin-Demonstration in Moskau - Nawalny Festnahme
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A cewar kafafan yada labarai na Rasha an kama dan adawar ne ana tsakiya da gangamin adawar da ya samu halartar dubban masu adawa da shugabancin Putin.

A cewar wani jami'i da ke aiki tare da Navalny dubban mutane ne za su fita zanga-zangar a birane 90 a fadin kasar don nuna adawa da sake zaben shugaban na Rasha a karo na hudu, inda shugaban zai rantsuwar kama aiki a ranar Litinin. 'Yan sanda sun kama mutane sama da 300 a fadin kasar bayan fitarsu wannan zanga-zanga a cewar 'yan fafutika.