'Yan sanda 1,500 a birnin Kwalan saboda tsaro
December 12, 2016Talla
Kimanin 'yan sanda 1,500 ne za a jibge a birnin Kwalan da ke a Yammacin kasar Jamus a wani bangare na shirye-shiryen bikin sabuwar shekara, sannan za a makala na'urorin daukar bayanai na kai kawo jama'a a dandalin da ke tsakiyar birnin dan kaucewa abin da ya faru a shekarar bara inda wasu matasa suka aikata abubuwan cin zarafi ga mata kamar yadda Juergen Mathies shugaban 'yan sanda a birnin ya bayyana.
Cikin matakan da za a dauka dai sun hadar da jibge jami'an rukuni-rukuni uku dauke da misalin 'yan sanda 300 da za a a ajiye a kusa da babbar majami'ar nan ta Kwalan cathedral kamar yadda Mathies a taron manema labarai, wanda mahalartansa har da Magajiyar garin birnin na Kwalan Henriette Reker da babban jami'in 'yan sanda su ka halarta.