Shari'a tsakanin 'yan Najeriya da Shell
December 18, 2015Wata kotun daukaka kara a kasar Holand ta bayyana a ranar Juma'an nan cewa wasu manoma hudu 'yan Najeriya na da dama a kasar su daukaka karar da suke yi ta kamfanin hakar albarkatun man fetir wato Shell cewa ya bata musu muhalli a Najeriya. Wannan hukunci dai na zama wanda ya kafa tarihi da aka samu hannun kamfanin na Shell a irin wannan shari'a.
Mai shari'a Hans van der Klooster ya ce kotun daukaka karar da ke a birnin Hague na da hurumi na sauraran wannan shari'a kan kamfanin da ke da reshe a Najeriya.
Manoman hudu da masunta daga yankin Niger Delta a Najeriya sun sami goyon baya ne na wata kungiya mai fafutikar kare muhalli mai suna Freands of the Earth wacce tun a shekarar 2008 ta gurfanar da wannan kamfani a kotun da ke da tazarar dubban kilomitoci daga inda lamarin gurbata muhallin ya faru.