1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta soke rijistar zabe a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
September 13, 2022

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriyar INEC, ta sanar da goge sunayen mutane fiye da milyan daya da dubu 100 daga cikin mutane fiye da milyan biyu da dubu 500 da suka yi sabuwar rijistar zabe a kasar

https://p.dw.com/p/4Gmzi
Najeriya | Zabe | Kati | Rijista
Mutane da dama dai sun yi rijistar zaben a Najeriya, cikin wahalaHoto: AFP/Getty Images/P. Utomi Ekpei

Hukumar Zaben mai Zaman Kanta a Najeriyar INEC, ta ce ta dauki matakin goge sunayen ne kasancewar sun lalace sakamkon matsaloli wajen rijistarsu. Hakan dai na nuni da cewa 'yan Najeriya kimanin miliyan daya da dubu 300 ne kacal, za su dace da shiga sabuwar rijistar zaben. Wannan matsala dai ta sanya nuna damuwa, kasancewar za ta hana adadi da dama yin zabe duk da cewa sun kai shekaru 18 da haihuwa. Tsaftace kundin rijistar masu kada kuri'ar dai, na zaman wajibi a tsarin dokar Najeriya kafin gudanar da babban zaben da ake shirin yi a 2023. Wannan adadi na fiye da mutane milyan daya da dubu 100 da hukumar zaben ta goge suyanensu daga rijistara masu zaben dai, wadanda suka yi rijista ne sababbi a tsakanin 28 ga watan Yunin 2021 zuwa 14 ga watan Janairun bana.

Najeriya | Zabe | Rijista
Mutane da dama a Najeriya, ba za su samu damar yin zaben 2023 baHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Bayan kwashe dogon lokaci ana wahala da gwagwarmaya wajen yin rijistar da har sai da kungiyoyin kasa da kasa da masu rajin kare dimukuradiyya a Najeriya suka sanya baki domin kara wa'adin yin rijistar, inda aikin ya zama babban jidali ga mutane da dama da suka kai shekaru 18 ne aka fuskanci wannan matsala a yanzu. Tuni kungiyoyin rajin kare hakin dan Adam suka mayar da martani a kan lamarin, sanin muhimmancin damar yin zabe ga 'yan kasa da suka kai shekaru 18 da haihuwa. Da alamu dai akwai sauran aiki a gaba, domin har yanzu akwai sauran wadanda aka yi wa rijista a zangon karshe da ake aikin tsaftace rijistarsu. Wannan dai na nuna akwai yiwuwar kara samun wani adadi na wadanda za a goge daga kundin masu kada kuri'ar, cikin adadin da hukumar ta sanar na sama da 'yan Najeriya milyan 10 da ta yi wa rijistar a kasar.