Masar: Shekaru 10 na hambarar da gwamnatin Mohammed Mursi
July 3, 2023Shekaru 10 bayan kifar da gwamnatin 'yan uwa Musulmi ta Masar a karkashin jagorancin Mohammed Mursi, har yanzu yan kasar na kewar manufofinsa da duba gurbin da kungiyarsa ta bari, duk da dubban magoya bayansa da ke daure. Har yanzu sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohammed Mursi, ba su cika galibin manufofin da hambararren shugaban ya sakawa gaba da ya taba fayyacewa a guda daga cikin jawabansa.
"Dole mu noma abincinmu mu hada magungunanmu da kanmu mu kera wa kanmu makamai, cimma wannan burin na bukatar bunkasa masana'antu da inganta noma da zuba isasshen jarin da zai inganta ilimi tamkar irin na kasashen yammacin duniya da na Chaina koma fiye da haka. Ba zai taba yiwuwa ba muddin ba mu yaki cin hanci da rashawa ba, muddin sojoji ba su tsame hannunsu a fagen siyasa da tattalin arziki, sun koma barikokinsu ba."
Za mu ba da fansar jini da jikinmu
"Dole a ba wa dan kasa cikakken yancinsa na dan kasa, kana kosar da shi shi ne 'yancin farko da ba wa kwakwlwarsa damar yiwa kanta ingantaccen zabi. Ba za mu taba zama 'yan amshin shatan wasu kasashen ba, ba za mu raga wa duk wani wanda ya nemi ya keta hurumin kasarmu ba, ba za mu lamunta a rage mana koda digo daya ne a kasarmu na ruwan kogin Nilu ba, za mu ba da fansar jinin jikinmu don kwato shi wannan 'yanci, in ji hambararren shugaban Masar Mohammed Mursi."
Karin Bayani: Tarihin hambarren Shugaba Mohamed Mursi na Masar
Shekaru 10 da wannan jawabin na marigayi Mohammed Mursi, darajar kudin Masar ya karye da kaso 300 cikin dari, talauci da zaman kashe wando ya karu, yancin fadin albarkacin baki a kasar ya ragu har ta sa kasar ta zama ta kusan karshe a jerin kasashen duniya wajen tauye yan jarida da masu fafutuka da tarin dubban firsunonin siyasa, bashin da ake bin kasar ya haura da kaso kusan 200 cikin dari da gina mashingin ruwa kan kogin Nilu da Habasha ta yi tare da saryantarwa da tsibiran Snafir da Tehan da Masar ta yiwa Saudiyya, duk wadannan sun sanya yan kasar na siffanta kawar da Mursi da sojoji suka yi da mummunar annoba da ta kassara mulkin mafi tausayawa talakawa da ke neman ganin kasar Masar ta tsaya da kafafuwanta.
An soma kada gangar siyasa
A yanzu gangar siyasa ta fara kadawa a Masar, duk da rage-ragen da ake tabbatar da cewa shugaba Abdel-Fattah el-Sissi ya yiwa kungiyar yan uwa Musulmi da shi kansa tsohon tsohon shugaban Masar Mohammed Mursi, da wasu jagororin kungiyar suka mutu a gidan yarinsa, baya ga wasu jagororin kungiyar dubu 60 da ke tsare ga dukkan alamu akidu da manufofin kungiyar ba su mutu ba, yadda wasu matasan kungiyar ke son fakewa a asirce su tsaya takara a matsayin yan majalisu a zaben da ake shirin yi na da gaba, wasu masu adawa da kungiyar sun fara yin kiraye-kirayen da kar a bari kai labari.
Karin Bayani: Jana'izar Mohamed Morsi
Masana kamar su Tharwat Al-Kharbawy, kwararre kan kungiyoyin Islama na cewa sojojin da suka yi juyin mulki a Masar sun kashe maciji ne ba tare da sare kansa ba, inda ya ce "Duk da cewa a tarihi ba su taba yin rauni kamar a wannan karon ba, har yanzu akidarsu na nan, kuma tana naso a cikin al'uummar kasar nan, har yanzu mutane na da imanin cewar ba adalci irin na mulkin tafarkin musulunci da yan uwa Musulmi ke tallatawa, kuma shi ne zai magance matsalolin tattalin arzikin da kasarsu ke fuskanta."