1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Majalisa a Najeriya na barazanar tsige shugaban ƙasa

July 20, 2012

Shugaba Goodluck Ebele Jonathan na Najeriya na fuskantar barazanar rasa madafun ikon ƙasar bisa zarginsa da gaza aiwatar da kasafin kuɗin bana yadda ya kamata

https://p.dw.com/p/15cF3
©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

A wani abun dake zaman martanin ta ga barazanar 'ya'yan majalisar wakilan Najeriya na kaiwa ga tsige shugaban ƙasar kan rashin iya aiwatar da kasafin kudin ƙasar, fadar gwamantin ta Aso Rock ta ce ba matsala ba haufi ga ƙoƙarin 'yan majalisar na neman ganin aiwatar da kasafin kamar yadda ya dace

A baya dai sun zamu sanda ta barazana a hannun majalisar Tarrayar Najeriya, sun kuma yi nasarar tabbatar da tasirin ta bisa tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo da ya sha fuskantar barazanar tsigewa a tsakanin 'ya'yan majalisar wakilan kasar.

To sai dai kuma daga dukkan alamu, tsohuwar dabarar tana shirin tasowa ga wakilan da suka kalli idon shugaban kasar suka shaida masa rashin gamsuwar su da yanda kasar ta Najeriya ke ƙoƙarin aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar na bana.

'Yan majalisar dai sun zargi gwamantin da gaza fitar da kuɗi domin aiyyuka duk da share tsawon kusan wattani bakwai a cikin shekarar da muke ciki.

Abun da kuma a cewar wakilan ke zaman babban laifin da ke iya kaiwa ga fara tunanin tsige shugaban dake cikin shekarar mulkin sa ta biyu da kuma ke kuma fuskantar barazanar a karon farko.

To sai dai kuma daga dukkan alamu sabon matsayin 'yan majalisar da suka fara takun saƙa a tsakanin su da fadar tun bayan kaddamar da binciken zare tallafin man fetur dai ya gaza harzuka fadar da tace tuni tayi nisa a kokarin cimma bukatun yan majalisar a cewar Dr Rudean Abati dake zaman kakain fadar

“Ga kokarin aiwatar da kasafin kudi kamar yadda ya kamata inajin yan majalisa da gwamanti na Magana ne da baki guda ina cewar shugaban kasa da 'yan majalisa na da tunani iri guda ba wata matsala kuma aiwatar da kasafin yayi nisa kuma yana kara samun cigaba. A iya cewar akwai yan batutuwa a wasu daga cikin bangarorin kasafin, amma dai ana yin namijin ƙoƙari kuma shugaba jonathan da kansa ne yake lura da aiwatar da kasafin kudin kamar yadda ya kamata.”

Duk da cewar dai yan majalisar sun kai ga bada wa'adin zuwa watan jibi na satumba domin sauyi dai majiyoyi sun ce rikicin kasafin, nada ruwa da tsaki da aiyyukan raya ƙasar yan majalisar da gwamantin tayi watsi dasu duk da kasancewar su cikin kasafin dake fuskanatar mummunan karancin kudi da muguwar siyasa a cikinsa.

national assembly.jpg
Hoto: DW

Siyasar da ke tattare da kasafin kuɗin

Siyasar kuma dake kallon fadar watsi da daukacin matakan da majalisar ke dauka da kuma suka hada da sake dawowa da shugabar hukumar kula da kasuwar hannun jarin kasar, sannan kuma da mantawa da alkawrinta na fara tuhumar masu ruwa da tsaki da badakalar tallafin man fetur tun daga wannan mako kamar yadda ta alkawarta tun da farko.

Ana dai kallon shi kansa wa'adin na satumba day a nemi aiwatar da kaso 100 cikin dari na kasasfin na naira trilliyan 4, 887 da ke zaman da kamar wuya a matsayin kokari na tsorata shugaban da sauya tunanin sa ga rashin biyayyar umarnin majalisar,

Burin kuma da daga dukkan alamu ya kama hanyar cika tare da fadar kaucewa duk wani kokari na fito na fito, ga dai abating

Eh akwai Magana game da aiwatar kasafin kudi inda Majalisar wakilai ke cewar kokarin aiwatar da kasafin kudi bashi da inganci. Kuma in har ba akai ga aiwatar da kasafin dari cikin dari ya zuwa watan satumba to kuma majalisa zata dauki wasu matakai kan shugaba jonathan. Abun da nake son in fada shine lallai babu wata matsala ga tunanin day an majalisar ke kokarin tabbatarwa.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabuwar gwagwarmayar iko a tsakanin fadar da hankalin ta ke rabe tsakanin kwantar da rikici na tsaro da zaman lafiya da kuma yan majalisar dake ƙoƙarin ƙwato 'yancin su a hannun bangaren zartarwa, na neman ƙara yamutsa gashin baki a tsakanin bangarorin biyu.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu