'Yan jaridun Turkiyya sun yi watsi da zargin ta'addanci
July 24, 2017Da dama daga cikin 'yan jaridun sun shafe kusan sama da watanni takwas a tsare ba tare da gurfanar da su a gaban kuliya ba. Tun bayan yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Racep Tayyip Erdogan da bai yi nasara ba a shekara ta 2016, 'yan jaridu da dama na cikin takunkumin rashin samun damar gudanar da aiki a fadin kasar.
'Yan jaridu a Turkiyya dai sun gudanar da ranar 'yancin 'yan jaridu ne a lokacin da ma'aikatan jaridar da ke adawa da gwamnatin kasar 17 ke gaban alkali. Idan dai gwamnatin na Turkiyya ta yi nasarar cimma wannan kara, 'yan jaridun za su kasasnce a gidan sarka na kusan sama da shekaru 43. To sai dai irin wannan mataki da Turkiyya ke dauka a kan 'yan jaridu, na ci gaba da ja mata karan tsana daga sauran kasashe mambobin kungiyar Tayayyar Turai da ke kafa hujja da yunkurin take 'yancin fadin albarkacin baki.