1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan tawayen Huthi sun kai wa Saudiyya hari

March 26, 2021

Gwamnatin kasar Saudiyya ta ce an harba makami mai linzami zuwa daya daga cikin cibiyoyin manta, harin da ta zargi 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen da kai wa.

https://p.dw.com/p/3rEoH
Saudi-Arabien Ölförderung zweite Version
Hoto: AP

Harin na zuwa ne a lokacin da kasar ta Saudiyya ke cika shekaru shida cif da shiga yakin basassar Yemen. Jami'an sojin kasar sun ce an kai hare-haren ga yankin Jizan da ke Kudu maso yammacin Saudiyar da ke kusa da iyakar kasar da Yemen. 


A wata sanarwa da 'yan tawayen Huthi da ke da goyon bayan Iran suka fitar ta kafar talabijin, sun dauki alhakin kai harin da jirage marasa matuka 18 da kuma makamai masu linzami a cibiyar man kasar da kuma sansanonin soji da ke Damman da Najran da Asir. 

Kakakin mayakan na Huthi Yehia Sarie ya ce a shirya suke su kai wasu munanan hare-hare nan da dan wani lokaci. Kasar Saudiyya dai na fuskantar karin hare-hare makamacin wannan tun bayan tayin tsagaita wuta da ta yi wa 'yan tawayen a baya-bayan nan.