Harin rokoki ya kashe sojojin Yemen
January 7, 2020Talla
Wannan hari shi ne karo na biyu cikin mako daya bayan harin farko da ya kashe sojoji biyaar a watan karshen shekarar 2019. Duk da shiga yakin da kasar Saudiyya ta yi a 2015 'yan tawayen Houthi na rike da riko da babban birnin kasar Sanaa da wasu yankun arewacin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya na kwatanta yakin Yemen a matsayin yaki mafi muni da ya gallaza rayuwar fararen hula bayan da yakin ya kashe dubban mutane miliyoyi suka yi gudun hijira.