1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin yakin kasar Moroko ya yi batan dabo a Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 11, 2015

'Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun yi ikirarin kakkabo wani jirgin yaki na rundunar taron dangi da Saudiya ke jagoranta domin kai hare-hare a kasar.

https://p.dw.com/p/1FOFi
Hare-haren Saudiya da kawayenta a Yemen
Hare-haren Saudiya da kawayenta a YemenHoto: Reuters/M. al-Sayaghi

Ikirarin nasu dai na zuwa ne jim kadan bayan da kasar Maroko da ita ma ta bi sahun masu luguden wutar a kasar ta Yemen, ta sanar da bacewar wani jirgin saman yakinta a Yemen din. Kafar yada labarai ta 'yan tawayen na Houthi Al-Masirah ta ruwaito cewa jami'an tsaron sararin samaniyarta sun kakkabo jirgin yakin ne a Wadi Nushur da ke gundumar Saada, yankin da 'yan Houthi ke da karfin iko. Sun kuma nuna hoton bidiyo na abin da suka bayyana da barakuzan jirgin da suka kakkabo din kewaye da shi kabilun yankin na ta shewa da nuna farin cikin samun nasara.