SiyasaAsiya
Ana ci gaba da tserewa daga Afghanistan
August 27, 2021Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana tsammani fiye da 'yan gudun hijira rabin milyan sun tsere daga kasar Afghanistan tun lokacin da mayakan Taliban suka kwace madafun ikon kasar. A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar kimanin mutane 515,00 za su fice daga kasar zuwa karshen wannan shekara ta 2021. Amma babu tabbacin yadda yanayi zai kasance a cikin kasar saboda rudanin rashin inda aka dosa.
Babu gagarumin dandanzon masu neman fiyewa daga kasar, amma tuni dubban mutane sun fice ta iyakokin kasar ta Afghanistan da kasashen Tajikistan, da Turkmenistan gami da Uzbekistan.