1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira miliyan 40 a duniya a 2015

Gazali Abdou TasawaMay 11, 2016

A shekarar ta 2015 kadai an samu sabbin 'yan gudun hijira miliyan takwas da dubu dari shida, daga cikinsu miliyan hudu da dubu dari takwas a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da kuma na Arewacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1IlRs
Äthiopien äthiopische Flüchtlinge Rückkehrer im Addis Ababa IOM Transit Center
Hoto: IOM Ethiopia

Sakamakon wani rahoto da hukumar kula da 'yan gudun hijira na cikin gida ta IDMC ta wallafa a wannan Laraba, ya nunar da cewa adadin mutanen da yake-yake suka raba da muhallinsu ya kai mutun dubu 40 a shekara ta 2015, kuma wannan adadi shi ne mafi girma da aka taba samu a duniya.

Rahoton ya ce a shekarar ta 2015 kadai an samu sabbin 'yan gudun hijira miliyan takwas da dubu dari shida, daga cikinsu miliyan hudu da dubu dari takwas a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da kuma na Arewacin Afirka.

Rahoton ya ce sama da kashi 50 daga cikin dari na mutanen da yakin ya raba da gidajansu 'yan kasashen Siriya da Yemen da Iraki ne, a yayin da sauran kashin 50 ya fito daga kasashen Afganistan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Kwalambiya da Jamhuriyar Demokradiyar Kwango da Najeriya, Sudan ta kudu da kuma Ukraine.

Rahoton ya kuma kara da cewa bala'o'i da suka auku, sun raba wasu mutanen sama da miliyan 19 da muhallinsu a kasashen Indiya, Chaina da Nepal a dai shekarar ta 2015.