'Yan fashi sun sace mutane 30 a Kaduna
June 9, 2018Wasu majiyoyi daban-daban sun nunar da cewar a ranar Jumma'a da magariba 'yan fashi da ke kan babrura suka sace mutane 22 a hanyar Birnin Gwari ciki har da wata mace da jaririnta. Dama kuma sun fara makamancin wannan fashi da safe inda suka sace mutane goma.
Satar mutane domin neman kudin fansa na dada karuwa a Arewacin Najeriya musamman a yankin kan iyakar Kaduna da jihar Zamfara, inda aka nunar da cewar daga nan masu aikata miyagun ayyuka da sace dabbobi ke fitowa. A farkon watan Mayu da ya gabata ma mutane kimanin 100 ne aka sace a cikin kwana biyu a kan wata hanya da ke yankin Birnin Gwari.
Shekaru 10 da suka gabata ne wadannan sace-sacen mutane suka samo tushe a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya mai arzikin man fetu, kafin ya bazu ko'ina a kasar, musamman a jihar Kaduna, inda ake sakosu bayan an biya kudin fansa.