'Yan bindiga sun kashe mutane 45 a jihar Kaduna
May 6, 2018Talla
Wannan kisan gilla ya biyo bayan mutuwar mutane 25 cikin wadansu hare-hare mabanbanta a arewacin Najeriyar cikin makon da ya gabata, a daidai lokacin da iyalan wasu mutane 13 ke cikin alhinin rashin su a jihar Zamfara sakamakon wani rikici tsakanin barayin shanu da kuma 'yan banga a Jihar Zamfara.
Yanayin tsaro dai na kara ta azzara a kasar lamarin da a halin yanzu ya haifar wa da shugaban kasar Muhammadu Buhari samun suka daga bangarori daban daban a ciki da wajen kasar. Bayan da matsanancin talauci ya addabi talakan kasar duk kuwa da cewar shugaba Buharin bai jima da bayyana aniyar sa ta sake neman takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019 ba.