1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Yan bindiga sun hallaka mutum 34

Ramatu Garba Baba
September 27, 2021

Yan bindiga sun hallaka mutum akalla 34 tare da raunata wasu da dama a wani hari da suka kai a kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura a Kudancin jahar Kaduna.

https://p.dw.com/p/40wq5
Nigeria Abuja | Sicherheitspersonal | Entführte Studenten
Hoto: Nasu Bori/AFP/Getty Images

A jahar Kaduna da ke arewacin Najeriya, daruruwa sun tsere daga gidajensu bayan wani harin 'yan bindiga da ya janyo asarar rayuka akalla 34, maharan sun kona gidaje bayan kashe-kashen jama'a a kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura na yankin kudancin jahar Kadunan.  Mr Samuel Aruwan wanda shi ne Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaron Jihar ta Kaduna ya tabbatar da aukuwar harin a wata sanarwar da ya fitar a yau din nan.

An soma tuhumar wasu da ake zargin nada hannu a harin inji Aruwan, har wa yau a jiya Lahadin, wasu 'yan bindiga sun kai hari kan masu ibada a wani coci da ke Kachia a jahar ta Kaduna inda suka kashe mutum guda da raunata wasu da dama. 

Rahotanni na cewa jama'a na tserewa saboda fargabar ramuwar gayya, sai dai an jibge jami'an tsaro a yayin da gwamnan jahar Mallam Nasiru el-Rufai, ya umurci Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jahar, da ta gaggauta kai ma wadanda harin ya rutsa da su kayayyakin agaji. 

Daruruwan Jama'a ne yanzu haka ke gudun hijira a yankin kudancin Kaduna sakamakon karuwar hare-haren 'yan bindiga da rigingimun masu nasaba da addinai tare da kabilanci