1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'yan Afruka sama da 200 suka nutse ruwa a gaɓar Yemen

December 18, 2007
https://p.dw.com/p/CdH3

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya tace aƙalla yan Afirka 200 ne suka rasa rayukansu ko kuma suka ɓace bayan kwale kwale guda biyu da suke ciki sun nutse cikin ruwa a bakin iyakokin ƙasar Yemen a ƙarshen mako.Rahotanni sunce ɗaya daga cikin kwale kwalen yana ɗauke ne da mutane 148 ya kuma nutse ne a ranar Asabar. Ɗaya kwale kwalen kuma dake ɗauke da fasinjoji 270 ya ci karo ne da wani dutse cikin teku a ranar Lahadi a ƙoƙarin matukansa na kaucewa jamian tsaro na Yemen. Fasinjoji 173 ne kaɗai suka iya yin iyo zuwa bakin gaɓa,sauran kuma yawancinsu mata da yara ƙanana har yanzu ba a ji ɗuriyarsu ba.