1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain: Shahara a noman strawberry

June 22, 2021

Kimanin tan dubu 300 na strawberry lardin Huelva da ke kudancin kasar Spain ke sayarwa duniya, musamman kasar Jamus. Wannan na faruwa da taimakon 'yan ci-rani daga kasar Maroko da kuma wasu kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/3vNNP
Marokko Saisonarbeiter auf einem Erdbeerfeld
'Yan Moroko da sauran ksashen Afirka, na aikin girbe strowberry a SpainHoto: Getty Images/AFP/A. Senna

Sai dai ana sukar yanayin da 'yan ci-ranin ke aiki da cewa keta hakin dan Adam ne. Su ma manoman na mayar da martani cewa masu kamfanonin Jamus da ke sayen kayan lambu, suna karya darajar farashinsa. Babbar gonar kayan lambu ta strawberry iya ganin mutum. Kanshinsa kuma sai wanda ya ji. A kan hanyar cikin gona akwai karamar motar daukar kaya mai na'urar sanyaya abinci. A wani bangare na gonar akwai mutane 24 daga cikin kimanin 'yan ci-rani dubu 100 da ke aikin girbe kayan lambun mai launin ja. Daga cikinsu akwai 'yar Maroko mai suna Fatima: "Akwai wahala a  Maroko. Ma'aikacin gona da ke girbe amfani ya kan samu Euro shida da Centi biyar a rana, amma a nan Spain mu kan samu fiye da Euro 40. Ko da yake ana samun bambancin yawan albashin, wasu su ce Euro 42 wasu kuma Euro 40. Babu tsari sosai na albashi."

Spanien Arbeitsmigration Europa Afrikanische Arbeiterin bei Erdbeerernte
Wata 'yar Moroko da ke aikin girbe strawberry a SpainHoto: Getty Images/AFP/C. Quicler

Sai dai Manuel Reina na kungiyar manoma ya ce ba a nuna bambanci tsakanin ma'aikatan, yana mai cewa a kan ba su muhalli kyauta, koda yake wakilan kungiyoyin ma'aikata irin su Jose Antonio Brazo ya ce shakka babu ana ci da gumin ma'aikata 'yan ci-rani daga Afirka a gonakin na Spain: "Sannu a hankali suna kin biyan albashin da aka amince da shi. Wato abin nunfi, ana ci da gumin 'yan ci-rani. A kowane kauye a nan akwai mutumi-mutumin Nana Maryam da ake girmama ta, amma a hakikanin gaskiya kusan duka suna bautar kudi ne."

Wani bincike da cibiyar Löning mai nazarin ayyukan kwadago masu dorewa a Berlin ta yi, ya tabbatar da cewa sau da dama ana biyan masu aikin girbe kayan amfanin gonan albashi mafi karanci. Sai dai manomi Manuel Reina ya ce su sana'arsu na tattare da kasada, suna tabka asara. A cewarsa, sau tari ma ba sa samun farashin da ya dace da hajjojinsu. Manoman dai ba sa sanin farashin da masu amfani da kayan ke biya. Sukan sayar da kilo guda na strawberry a kan Euro daya zuwa Euro daya da Centi 50, abin da a kantuna farashinsa ya kai Euro shida.