Yan adawar Yemen sun shirya bikin farin ciki
June 5, 2011Talla
Waɗanda ke adawa da manufofin gwamnatin Ali Abdallah
Saleh na Yamal sun bayyana cewar za su ɗauki dukkan
matakan da suka wajaba, domin hana shugaban dawowa gida
bayan karɓan magani a wani asibiti na ƙasar Saudiyya. Suna
masu danganta fitar da shi daga ƙasar da wani muhimmin
mataki da zai kawo ƙarshen so toka sa katsi da ake yi da
nufin raba shi da madafun iko. Ɗaruruwan mutane ne dai
suka fantsama akan titunan birnin Sana'a domin nuna farin
cikinsu da kai shugaba Saleh da ya ji rauni da kuma iya da
maƙarrabansa wajen ƙasar domin jiyya. Ya zuwa yanzu dai ba
a san wanda ke riƙe da ragamar mulki ba, kasancewar
shugaba saleh bai miƙata ga mataimakinsa kamar yadda
dokokin ƙasar suka tanada ba. Sai dai kakakin jam'iyar da ke
kan karagar mulki a Yemen wato Tarek El Chami ya bayyana
ma tashar telebijin ta Al arabiya cewar nan da kwanaki ƙalilan
shugaba zai dawo gida domin ci gaba da gudanar da harkokin
mulki. Rikici tsakanin Bangaren gwamanti da kuma mayanƙan
sa kai na ƙabilun ƙasar na ci gaba da ƙamari tun bayan
wargajewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka cimma.
Mawallafi:: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Yahouza Sadissou Madobi