1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Najeriya za su yi wa PDP taron dangi

November 13, 2012

Manyan jam'iyun adawar Najeriya guda uku sun fara tattaunawa da nufin kawo ƙarshen mulkin jam'iyar PDP a ƙasar.

https://p.dw.com/p/16i8L
Hoto: AP

A wani abun dake zaman sabon yunƙurinsu na kawo ƙarshen mamayar jam'iyar PDP mai mulki a tarrayar Najeriya, manyan jam'iyun adawar ƙasar uku sun ce sun buɗe tattaunawa da nufin haɗewa wuri guda domin tunkarar PDP a zaɓukan ƙasar masu zuwa.

Sun dai share shekaru ɗai ɗai har 13 suna ji a jiki ga jam'iyun adawar tarrayar ta Najeriya dake zaman jira na alƙawarin PDP mai mulkin ƙasar na shekaru 60 kafin iya kaiwa ga kyale ɗana mulki a tsakaninsu.

To sai dai kuma daga dukkan alamu ba su karaya ba a gwagwarmayar da ta kai su ga sabon tunanin gamewa wuri guda da nufin gwada sa'ar ganin bayan PDP da ta mamaye ɗaukacin fagen siyasar Najeriya ya zuwa yanzu.

Babban ƙalubale a gaban 'yan adawa

Aƙalla manyan jam'iyun adawar CPC da CAN da kuma ANPP ne suka amince da sake ƙoƙari na gamewa wuri guda aƙalla shekaru uku kafin babban zaɓen ƙasar na gaba.

A wani abun dake nuna irin girman ƙalubalen dake gabansu da kuma irin siyasar da kasar ke shirin fuskanta a gaba.

Wahlen Nigeria Attahiru Jega
Attahiru Jega shugaban hukumar zaɓe, ana zargin hukumarsa da goyon bayan PDPHoto: AP

To sai dai kuma irin wannan ƙoƙari ya ci tura 'yan wattani kafin zaɓen shugaban ƙasar na shekara ta 2011 sakamakon kiki-kakar da ta mamaye ƙokarin tsaida ɗan takara da ma rabon ragowar muƙaman siyasar in an kai gaci.

Abun kuma da a cewar Mallam Mustapha Salihu dake zaman mataimakin shugaban jam'iyar CPC na ƙasa ba gaskiya ba ne.

PDP ta mamaye fagen siyasar Najeriya

Tarko irin na hukumar zaɓe ko kuma zagon ƙasar jam'iyar PDP dai daga dukkan alamu 'yan adawar Najeriya na da jan aiki a ƙoƙarin ganin bayan PDP jam'iyar dake da kusan kaso 70 cikin 100 na zaɓaɓɓun muƙaman ƙasar ta Najeriya da kuma daga dukkan alamu ba ta shirin sauka ga ci-gaban mamayar harkokin siyasar ƙasar na lokaci mai tsawo.

To sai dai kuma a cewar Dr. Jibo Ibrahim shugaban cibiyar raya demokraɗiyya da ci-gaba a ƙasar sannan kuma mai bin diddigin harkokin siyasar Najeriya 'yan adawar ƙasar na iya nasara in har sun gano bakin zaren a ƙoƙarin nasu.

Presidential candidate of Action Congress of Nigeria, Mallam Nuhu Ribadu holds the broom to flag off his presidential campaign rally at the City Centre in Dutse, Jigawa State, on February 28, 2011. Thousands of supporters of the Action Congress of Nigeria waved their brooms, the party's symbol to cheer former Economic and Financial Crime Commission (EFCC) leader and presidential candidate of the party Mallam Nuhu Ribadu, as he began his presidential campaign rally in Dutse, Jigawa State. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Nuhu Ribadu ɗaya daga cikin kusoshin adawaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Najeriya dai ta share shekaru 13 na sake dawowar demokraɗɗiyyarta tana fuskantar barazanar babakeren jam'iya ɗaya tilo, abun kuma da sannu a hankali ke raguwa tare da ƙara ƙarfin 'yan adawar ƙasar da ya zuwa yanzu ke da aƙalla jihohi tara a cikin 17 ɗin dake sashen kudancin ƙasar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani