'Yan adawan Yemen sun bayar da kai bori ya hau
April 26, 2011'Yan adawan ƙasar Yemen sun amince da shirin da majalisar tuntuɓar juna ta ƙasashen yankin Gulf ta tsara, wanda ya tanadi shubaga Ali Abdallah Saleh ya miƙa ragamar mulki ga mataimakin sa nan da wata ɗaya. Ko da shi ke dai har yanzu masu neman sauyin ba su rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da aka cimma ba, amma kuma sun yi alƙawarin shiga cikin gwamnatin haɗaka da za a kafa.
Bisa ga wannan shirin dai, ɗaya daga cikin masu neman sauyin gwamnati ne zai ja ragamar mulkin ƙasar daga ƙarshen watan mayu har zuwa bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa nan da watannin uku masu zuwa. Kana sassa biyu sun amince cewar ba za a gurfanar da shugaban Ali Abdallah saleh gaban ƙuliya ba, duk da far wa fararen hula da ke ƙin jinin gwamnatinsa da yayi.
Sai dai masu zanga-zangar sun sha alwashin ci gaba da gudanar da boren ƙin jinin gwamnati har sai sun tabbatar da cewar an aiwatar da tsarin da sassa biyu suka amince da shi. Sama da mutane 130 suka rasa rayukansu a ƙasar ta Yemen tun bayan fara zanga-zangar neman sauyi a watan janairu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman