1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawan Chadi na a shirye domin tattauna

Salissou BoukariAugust 20, 2016

A daidai lokacin da suke shirin shiga kafar wondo guda gwamnatin kasar daga mako mai zuwa, 'yan adawan kasar Chadi sun ce a shirye suke su tattauna da bangaran gwamnati.

https://p.dw.com/p/1JmCW
Tschad N'djamena Saleh Kebzabo (L) and Ngarlejy Yorongar
Saleh Kedzabo da Ngarlejy YorongarHoto: Getty Images/AFP/G. Cogne

'Yan adawan kasar Chadi sun yi kira ga tattaunawa da ta shafi kowa da kowa a kasar, tare da bangaran gwamnati kwanaki goma bayan rantsar da shugaban kasar Idriss Deby Itno a wani sabon wa'adin mulki na biyar. Cikin wata sanarwa da sunan gamayyar jam'iyyun adawan kasar, madugun 'yan adawan na Chadi Saleh Kedzabo ya ce a shirye suke da su zauna a kan taburin tattaunawa da gwamnati, amma kuma tare da halartar masu shiga tsakani na kasa da kasa da ke tallafa musu yau da kunlu a fuskar ci gaban demokaradiyya.

A hannu daya kuma 'yan adawan sun shirya zanga-zanga daban-daban a kasar, inda a cewar madugun 'yan adawan na Chadi wannan mako mai zuwa ba zai kasance na hutu ga bangaran gwamnati ba, inda ya ce za su yi kokawa domin yakar yadda jam'iyya mai mulki ta MPS ke jagorantar kasar.