1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan adawa sunce babu gudu babu ja da baya a Yukrain

January 24, 2014

A karon farko, an sami mace-mace a rikicin jamhuriyar Yukrain, tsakanin yan adawa da shugaban kasar Viktor Yanukowitsch mai samun goyon bayan Rasha.

https://p.dw.com/p/1Aw4q
Hoto: Reuters

Ranar Laraba lokacin dauki ba dadi mafi muni ya zuwa yanzu, yan sanda sun yi kokarin tarwatsa yan zanga-zanga dake neman Yanukowitsch ya sauka daga mukaminsa, inda har akalla mutane hudu suka rasa rayukansu.

Yan adawar a jamhuriyar Yukraine suna zanga-zanga ne domin nuna kyamarsu ga manufofin shugaban kasar mai ci a yanzu, Viktor Yanukowitsch na kara kusantar Rasha, yayin da suka ce al'ummar kasar sun fi kaunar ganin kasarsu ta kusanci kasashen yamma. Lokacin jawabi a dandalin Maidan, wanda aka maida shi dandalin yanci a Kiew, shugaban yan adawa Vitali Klitschko yace shi da takwarorinsa yan adawa a shirye suke game da tattaunawa da Yanukowitsch. Klitschko ya shaidawa dubban masu sauraronsa a dandalin cewar shugaban kasar yaki yarda da bukatunsu, inda yace babu wani shiri na gudanar da sabon zabe kamar yadda suka nema, yayin da majalisar dokoki ita ce take da ikon yanke shawara a game da yiwuwar murabus na shugaban kasa. Tun da rana a jiyan Yanukowitsch ya gana da wakilan yan adawa a fadarsa, cikinsu har da Vitali Klitschko da tsohon ministan tattalin arziki Arseni Jazenjuk da kuma dan kishin kasa Ole Tjahnibok. Daga baya Klitschko ya nunar da cewar:

"Sojojin gwamnati suna da shirin amfani da karfi domin kwashe yan zanga-zanga daga dandalin Maidan. Zamu yi iyakacin kokarinmu domin ganin hakan bai yiwu ba, sa'annan a gobe, idan har shugaban bai amince da bukatunmu ba, zamu sake taruwa, saboda bamu da wani zabin da ya wuce wannan."

Ranar Alhamis kuwa, dubban yan adawa suka sake haduwa a dandalin, inda sukai ta kona tayoyin mota da duk abin da suka ci karo dashi, domin baiyana karar su ga dokar da ta fara aiki tun misalin makonni biyu da suka wuce, wadda ta haramta zanga-zanga a kasar ta Yukraine. Halin da ake ciki a kasar ya kara kazamcewa, bayan da labari ya bazu cewar yan sanda sun kama karin yan adawa. Rasha, kasar da yan adawar suke zargin ta zama ita ce wuka, ita ce nama a harkokin mulkin Yukraine, ta baiyana zargin cewar kasashen ketare suna shisshigi a harkokin cikin gidan wannan kasa. Kakakin shugaban Rasha, Vladimir Putin yace kasar sa tana bakin cikin ganin cewar kasasahen ketare suna da hannu a halin da ake ciki na rashin hankali a kasar ta Yukraine. A daya hannun, Pirayim ministan kasar, Mikola Asarow yace:

Ukraine Proteste in Kiew 23.01.2014 Klitschko
Shugaban yan adawa, Vitali KlitschkoHoto: Reuters

Duk abin da ya samu a kasarmu, da farko laifinsa yana kan jam'iyu ne na adawa, wadanda sune suka da alhakin jefa kasar cikin wannan matsayi. Nan da yan kwanaki masu zuwa ya kamata yan adawar su fito fili su baiyana matsayinsu, ko suna goyon bayan wadannan da basa komai sai haddasa tashin hankali da zub da jini, masu ra'ayin rikau da haddasa rigima. Idan haka ne, ya kamata su fito fili suce suna goyon bayansu. Idan kuma har wadannan masu neman tada zaune tsaye basu daina ba, gwamnati bata da zabi illa tayi amfani da karfi, kamar yadada doka ta tanada.

A halin da ake ciki kuma, tsohon shugaban Rasha, Michail Gorbatschow yayi kira ga shugaban rasha mai ci, Vladimir Putin da shugaban Amirka Barack Obama su taimaka a sami zaman lafiya a kasar ta Yukraine. Kungiyar hadin kan Turai a Bruessels tace tana nazarin yiwuwar dorawa Yukraine din takunkumi, bayan da rikicin kasar ya kai matsayin da aka fara samun asarar rayuka yanzu.

Ukraine Kiew Gespräch Präsident mit Opposition
Ganawar shugaban kasa da yan adawa a YukrainHoto: picture-alliance/dpa