Chadema, ta yi kira ga magoya bayanta da su fito yin bore
July 31, 2021Cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Asabar a birnin Dar es Salam , jam'iyyar Chadema ta kara da cewa ta shigar da kara kan "ta'addanci" da ake zargin shugabanta da aikatawa. An dai cafke Freeman Mbowe da wasu jiga -jigan jam'iyyar Chadema a garin Mwanza tun kwanaki goma da suka gabata a lokacin da suke shirin gudanar da gangami don neman a yi garambawul ga kundin tsarin mulkin Tanzaniya.
Tuni dai wata kotu ta tuhumi Freeman Mbowe mai shekaru 59 a duniya da zargin hada kai da 'yan ta'adda tare da samar da kudade gudanar da munanan ayyukansu-laifukan da ba sa bayar da damar a yi belinshi.
Wannan kame Mista Mbowe ya tayar da damuwa tsakanin kungiyoyi kare hakkin bil'adama da manyan kasashen yammancin duniya. Amirka ta bukaci shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, wacce ta hau karagar mulki a watan Maris bayan mutuwar John Magufuli, da ta tabbatar da kare 'yancin dukkan 'yan kasa.