´Yan adawa a Burma sun yi watsi da tayin gwamnati na yin sulhu
October 5, 2007Talla
Wakilin MDD na musamman a kasar Burma ko Myanmar Ibrahim Gambari ya yiwa babban sakataren majalisar Ban Ki Moon bayani akan halin da ake ciki a kasar dake yankin kudu maso gabashin Asiya. A ziyarar da ya kai kasar kwanakin nan Alh. Gambari ya gana da shugabannin gwamnatin mulkin soji da kuma shugabar ´yan adawa Aung San Suu Kyi wadda ake yiwa daurin talala. Manufar ziyarar dai shi ne shawo kan gwamnatin sojin da ta kawo karshen amfani da karfi wajen murkushe zanga-zangar nuna adawa da ita. Alkalumman da ´yan adawa da suka yi kaura daga kasar suka bayar yayi nuni da cewa mutane kimanin 200 aka kashe sakamakon matakan karfi da ´yan sanda da sojoji suka dauka kan masu zanga-zangar. Gwamnati dai ta amsa cewa ta kame mutane dubu 2. A jiya alhamis ba zato ba tsammani gwamnati ta yiwa ´yan adawa tayin zama kan teburin shawarwari. To amma ´yan adawa sun watsi da wannan tayi.