1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yammacin Afirka: Sabuwar hanyar shiga Turai

August 26, 2024

Kimanin bakin haure 21,620 suka tsallaka daga gabar ruwan Afirka izuwa Tsibirin Canary da ke karkashin kasar Spain wanda ya zama sabuwar hanyar da 'yan gudun hijira suka bude don shiga Turai

https://p.dw.com/p/4jwCh
Flüchtlingsroute El Hierro
Hoto: Europa Press/AP Photo/picture alliance

Firimiyan Sipaniyan zai yi ziyarar ne a kasashen Mauritaniya, Senegal da Gambiya, wandanda ke bakin ruwan da bakin haure ke bi don tsallakawa daga Afirka izuwa Turai. Wannan dai ita ce ziyara ta biyu a bana da Pedro Sanchez ke kaiwa a Yammacin Afirka, wanda kuma ziyara ce da duk ke kokarin magance matsalar 'yan gudun hijira. Yayinda a da bakin haure ke ta bin kasar Libiya su shiga Turari ta kasar Italiya, amma a yanzu sakamakon yunkurin kasashen Turai na karfafa toshe hanyoyin da 'yan gudun hijiran suka saba bi, a yanzu sai ku bullo da hanyar shiga Turai ta tsibirin Canary. 'Y gudun hijiran dai kan tashi musamman daga gabar ruwan kashen Senegal da Maurtaniya. A cewar rundunar Frontex da ke tsaron gabar ruwan Turai, rundunar da aka kafa don hana bakin haure shiga Turai, tace a watannin bakwai na farkon bana kadai kimanin baki 'yan ci-rani 21,620 suka tsallaka daga gabar ruwayen Afirka izuwa Tsibirin Canary da ke karkashin kasar Spain.