SiyasaUkraine
Yakin Ukraine ya sa mutane miliyan 14 yin hijira
February 22, 2024Talla
Baya ga wannan adadi da ke wakiltar kashi daya cikin uku na al'ummar Ukraine da suka nemi mafaka a kasashe 11 na nahiyar Turai, da akwai karin wasu miliyan 3,7 da su kuma suka watsu a wasu sanssan kasar.
A lokacin da take sanar da wadanan alkaluma shugabar hukumar Amy Pope ta ce kawo yanzu mutane miliyan 4,5 sun koma gida bayan lafawar lamura a yankunansu, sai dai amma suna bukatar tallafi domin sake gina rayuwarsu. Manyan bukacin tsaffin 'yan gudun hijirar in ji Mme Pope sun hadar da guraren zama da kuma ababen more rayuwa.