Yakin neman zabe na kara zafafa a Najeriya
March 2, 2015Jam'iyyun biyu na PDP mai mulki da APC ta 'yan adawa da suka faro daga yarfai na siyasa da sunan neman magoya baya, a yanzu salon ya canza zuwa ga kai wa juna hari da bakaken maganganu na batanci har ma da kazafi na fatan mutuwa bisa zargin na babu gaira babu dalili, duk da sunan yakin neman zaben da ya kamata a ce a karni na 21 an manta da irinsa a Najeriyar. Na baya baya nan dai shi ne na zargin da PDP ta yi na bankado makarkashiya ta yarjejeniya a tsakanin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC Yomi Osibanjo kan cewar zai yi watanni shida ne ya sauka ya mika wa Bola Tinubu, ya zuwa APC da ta dage cewa ana kokarin rufe asusun wasu manyan 'yan jam'iyyar da suka yi masu kafar ungulu. Duka kalamai ne da babu shaidar tabbatar da faruwar hakan. To shin me wannan ke nunawa ne ga siyasar ta Najeriya? Barrister Mainasara Umar mai sharhi ne a kan al'ammuran yau da kullum a Najeriyar.
"Harkokin siyasa ya kamata tun farko su kasance suna dinke ne mace da namiji. Kamar daurin aure ne tsakanin mene ne ra'ayin jama'a da kuma ra'ayin jam'iyyun siyasa. Amma a Najeriya yanzu an shiga wani yanayi wanda yake tun da aka fara demokradiyya a kasar tun ma kafin 1960 yakin neman zabe bai taba kazancewa ba irin na wannan lokaci. An tashi daga mene ne zai jawo ra'ayin masu zabe, abokan takara sun zama abokan gaba a siyasar nan, ta yadda za ka ga ana fito da kalamai munana ta kafofin yada labarai wanda ba abu ne mai kyau ba".
Bisa ga la'akarai da irin sarkakiyar da ke tattare da zaben Najeriyar na wannan shekara da tun bayan daga shi ake nuna dar-dar da fatan a yi shi a wanye lafiya ba tare da fuskantar wata matsala ba, abin da ya kai ga wasu kungiyoyin kasashen duniya shiga cikin lamarin ta hanyar bada shawara. Amma ga Dr Mohammed Abba dattijo mai sa ido a kan harkokin kasa ya ce abu daya ne ya kamaci al'ummar Najeriyar a yanzu.
"Babban abin da ya kamaci dukkannin ‘yan Najeriya shi ne mu yi hakuri da junanmu, mu kuma roki Allah ya shiryemu, ya maida mu a kan hanyar da za mu kara wa kasar nan daukaka da daraja. Domin in ba mu hakura ba za mu rasa abubuwan da muke nema duka, don ko abokan zamanmu na waje ba za mu same su ba kowa zai guje mu, to idan an gujemu kuwa komai zai kara lalacewa".
Damuwar kara fadawa cikin wannan yanayi da ke nuna tamkar babu mai shiga tsakani musamman a tsakanin jam'iyyun APC da PDP ya sanya tambayar hatsarin da ke tattare da hakan. Tun da dadewa dai ake gargadi ga makomar Najeriyar da ke sanya dole a sa ido domin ganin an gudanar da zaben lafiya, abin da ya sanya kwararru a wannan harka bayyana cewa masu furta irin wadannan kalamai su sani cewa tun kafin wannan lokaci akwai Najeriya kuma bayansu ma kasar za ta ci gaba da wanzuwa cikin aminci da ma kwanciyar hankali.