Yakin kasuwanci tsakanin China da Amirka
April 6, 2018Shugaba Trump na Amirka ya ce zai kuma kara wa kasar ta China wani sabon haraji na dalla miliyan dubu 100 kan kayayakinta da suke shigowa a kasar ta Amirka a matsayin sabon martani. Sai dai Da yake magana kan wannan batu ministan harkokin wajen kasar ta China Wang Yi, ya soke wannan mataki na Amirka inda yake cewa:
"Harkokin tattalin arziki na kasar Sin da na Amurka su na da alaka da juna, sannan bukatun bangarorin biyu duk na tafiya ne tare. Don haka Amirka ta yi rashin gaskiya idan ta ce za ta dauki matakin kare kanta ita kadai, alhali kasashen China da Amirka manyan kasashe ne da ta kamata su girmama juna."
Ministan harkokin wajen kasar ta China ya yi wadannan kalamai ne a birnin Mosko, yayin wani taron manema labarai da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov. Daga nashi bangare ofishin ministan harkokin kasuwanci na kasar ta China ya ce zai dauki dukannin matakan da suka dace kan wannan batu koma mi take zama ta zama tsakaninsu da Amirka.