1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da kyamar Yahudawa

Ramatu Garba Baba
October 13, 2021

Wakilai daga sassan duniya sun soma wani taron shawo kan matsalar kyamar Yahudawa da yanzu ke daukar sabon salo a shafukan sada zumunta na zamani.

https://p.dw.com/p/41cyH
Deutschland I Aktion gegen Antisemitismus I Synagoge in Gelsenkirchen
Hoto: Ina Fassbender/AFP

A wannan Laraba ake gudanar da wani taro na tuni da kisan kiyashin Yahudawa na Holocaust, sai dai mahalartar taron, sun yi amfani da ranar don jan hankulan duniya kan yakar annobar kyamar Yahudawa da ake yi a sassan duniya. Hasali ma makasudin taron shi ne, yakar annobar kyamar Yahudawa tare da ba su kariya a duk inda suke da kuma ba su 'yancin walwala.

Taron na kwana guda da kuma shi ne karo na biyu da ake irinsa, na gudana ne a kasar Sweden, ya kalubalanci masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani wajen yada manufar kin jinin Yahudawan, a wani lokaci a wannan Laraba, ake sa ran shata sabbin matakai da ake fatan za su taimaka a shawo kan matsalar.

Yahudawa kusan miliyan shida aka hallaka a lokacin yakin duniya na biyu, bincike ya nunar da cewa har ya zuwa yau dinnan, suna kuma ci gaba da fuskantar barazana iri-iri musanman tun bayan baiyanan shafukan sada zumunta na zamani inda ake rubuce-rubuce na kin jininsu.