1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da dillancin kayan maye a Najeriya

May 2, 2018

Kungiyoyin da ke yaki da shaye-shayen kayan maye a Najeriya sun yi murna da matakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar akan haramta shigowa da sarrafa maganin "Codein" baki daya a kasar, domin ceto rayukan matasa.

https://p.dw.com/p/2x34j
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture alliance/NurPhoto

Babu shakka dai wannan mataki da ministan kiwon lafiya a Najeriya Mr. Isaac Adewole  ya sanar na hana shigowa da sarrafa maganin Codein da samari da ‘yan mata da matan aure ke sha saboda hatsari ga lafiyar al'umma da kuma illolin da ke tattare da shi, hakan ya biyo bayan karuwar rahotanni daban-daban ne ta kafafen watsa labarai da koke-koken kungiyoyin da ke yaki da shaye-shayen kayan maye barkatai musanman ma dai a yankin arewacin Najeriya.

Minista Adewole ya ce daga yanzu ba za su sake amincewa ba wa duk wanda ya karya wannan doka ba komin matsayinsa, ya kuma nunar da cewa gwamnati za ta hada hannu da hukumar wayar da kan jama'a a Najeriya da hukumar kwallon kafa ta kasa da kungiyoyin malaman addinai da kungiyoyin matasa, da na mawaka domin tallata wannan shiri na gwamnati.

Ta hanyoyi da damar gaske ne dai matasan arewacin Najeriya ke anfani da su wajan samun kwalaben Codein domin sha, kuma wannan lamari ya fi tsananta ne tun daga matasa mazauna birane zuwa karkara.

Kalzium-TablettenKalzium-Tabletten
Wasu matasan kan shan kwayoyi barkataiHoto: Colourbox

Malam Lawal Maduru wanda aka fi sani da suna Malam Nigga, shi ne dai shugaba cibiyar gyara tarbiyyar matasa masu shaye-shaye a garin Kaduna arewacin Najeriya da ya yi murna da wannan mataki  ya ce zai rage lalata tarbiyar matasan.

Rahotannin sun nunar da cewa sinadarin da ke cikin ruwan maganin yana da alaka da hodar iblis da kuma garin hodar a-ji-garau. Haka zalika a wani binciken da masana muggan kwayoyi suka gudanar sun nunar da cewa yawancin masu shan kwayoyi na amfani da shi idan ba su iya sayen kwayoyin bugarwa masu dan karen tsada

Comrade Isa Gashi kwararren masani ne da ke yaki da masu fatauci da safarar kwayoyi a Najeriya ya ce arewa ce ta fi yawan mashaya kwayoyi, kuma yawanci matasa ne majiya karfi. Comrade  Isah ya ce kamata ya yi gwamnati da dukkanin sauran kungiyoyin al'ummar Najeriya su hada kai su yi wa wannan dabi'a taron dangi domin ceto al'umma.