1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki a Najeriya: An kai ƙarar shugaba Jonathan a kotun ICC

January 12, 2012

Wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam a tarrayar Najeriya sun kai ƙarar Goodluck Jonathan a kotun sauraren laifuffukan yaƙi saboda yadda jami’an tsaro suka afka wa masu zanga-zangar lumana tare da hallaka wasu da dama.

https://p.dw.com/p/13iPM
epa03046191 (FILE) A file photograph Goodluck Ebele Jonathan, President and Commander-in-Chief of the Armed Forces of the Federal Republic of Nigeria speaks during the general debate at the 66th session of the United Nations General Assembly at United Nations headquarters in New York, New York, USA, on 21 September 2011. Media reports state on 31 December 2011 that President Goodluck Jonathan has declared a state of emergency in areas affected by attacks from the Islamist group Boko Haram. Borders will be temporarily closed in the north-eastern states of Yobe and Borno, and central state of Plateau. EPA/JASON SZENES *** Local Caption *** 00000402928322 +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyoyin sun yi zargin cewa jami'an tsaron sun yi amfani ne da umurnin da shugaba Jonathan ya basu wajen buɗe wuta ga masu zanga-zangar lumana ta neman ‘yanci da ake yi a duk faɗin tarayyar Najeriya.

Rahotanni na nuna an hallaka mutane goma sha biyu a lokacin zanga-zangar nuna adawa da janye tallafin mai da gwamnatin Jonathan ta yi a matsayin goron sabuwar shekara amma Sifeta Janar na ‘yan sandan ƙasar Hafiz Ringim ya ce mutane uku kacal suka rasa rayukansu.

Saboda haka ƙungiyoyin fararen hula suka nemi kotun sauraren laifuffukan yaƙi ta duniya ta tuhumeshi gami da hukunta shi da duk wanda yake da hannu a wannan kisar gilla da ake zargin jami'an tsaron gwamnatin ƙasar sun yi akan talakawa a sassan jihohin ƙasar.

Alhaji Abba Muhammad Gwani shine shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bani Adama ta Civil Liberty Organisation CLO na jihar Gombe wanda kuma ya ba da dalilin ɗaukar wannan mataki na su a wannan lokaci.

People protest following the removal of fuel subsidy by the government in Lagos ,Nigeria, Monday, Jan. 9, 2012. A national strike paralyzed much of Nigeria on Monday, with more than 10,000 demonstrators swarming its commercial capital to protest soaring fuel prices and decades of government corruption in the oil-rich country. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Hoto: dapd

Wannan kuka nasu da suka miƙa na zuwa ne a dai-dai lokacin da ita kuma gwamnatin tarayyar take zargin ƙungiyoyin fararen hula da ‘yan adawa da tunzura talakawa wajen yin bore tare da tada hankula a faɗin ƙasar.

Sai dai masu fashin baƙi kamar Babangari Muktar na ganin gwamnatin ta rasa abin faɗa ne ganin al'ummar sun juya mata baya ga manufar da ake ganin wasu ƙalilan ne ke neman sai an aiwatar da ita.

Wasu ɓangarori kuma sun nemi a janye wannan zanga-zanga saboda halin rashin tsaro da ƙasar ta tsinci kanta a ciki sanadiyyar hare-haren da ake kaiwa na bama-bamai da bindigogi musamman a yankin Arewa maso gabashin Najeriyar.

Angry youths protest with a placard 'We are ready for civil war if the fuel price cannot come down' on the third day of nation wide strike following the removal of a fuel subsidy by the government in Lagos, Nigeria, Wednesday, Jan. 11, 2012. Nigeria;s government has warned an ongoing, paralyzing national strike risks anarchy in the oil-rich nation, as demonstrations over spiraling fuel prices and government corruption entered its third day Wednesday. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Hoto: dapd

Yanzu haka dai ala tilas an kafa dokar hana fita na tsawon awanni 24 a wasu jihohin ƙasar don magance tashe-tashen hankula da ake dangantawa da zanga-zangar lamarin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bani Adama suke cewa na fakewa da guzuma a harbi karsana ne.

Mawallafi: Mohammed Al'amin Suleiman
Edita: Mohammad Nasiru Awal