Yajin aiki a Najeriya: An kai ƙarar shugaba Jonathan a kotun ICC
January 12, 2012Ƙungiyoyin sun yi zargin cewa jami'an tsaron sun yi amfani ne da umurnin da shugaba Jonathan ya basu wajen buɗe wuta ga masu zanga-zangar lumana ta neman ‘yanci da ake yi a duk faɗin tarayyar Najeriya.
Rahotanni na nuna an hallaka mutane goma sha biyu a lokacin zanga-zangar nuna adawa da janye tallafin mai da gwamnatin Jonathan ta yi a matsayin goron sabuwar shekara amma Sifeta Janar na ‘yan sandan ƙasar Hafiz Ringim ya ce mutane uku kacal suka rasa rayukansu.
Saboda haka ƙungiyoyin fararen hula suka nemi kotun sauraren laifuffukan yaƙi ta duniya ta tuhumeshi gami da hukunta shi da duk wanda yake da hannu a wannan kisar gilla da ake zargin jami'an tsaron gwamnatin ƙasar sun yi akan talakawa a sassan jihohin ƙasar.
Alhaji Abba Muhammad Gwani shine shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bani Adama ta Civil Liberty Organisation CLO na jihar Gombe wanda kuma ya ba da dalilin ɗaukar wannan mataki na su a wannan lokaci.
Wannan kuka nasu da suka miƙa na zuwa ne a dai-dai lokacin da ita kuma gwamnatin tarayyar take zargin ƙungiyoyin fararen hula da ‘yan adawa da tunzura talakawa wajen yin bore tare da tada hankula a faɗin ƙasar.
Sai dai masu fashin baƙi kamar Babangari Muktar na ganin gwamnatin ta rasa abin faɗa ne ganin al'ummar sun juya mata baya ga manufar da ake ganin wasu ƙalilan ne ke neman sai an aiwatar da ita.
Wasu ɓangarori kuma sun nemi a janye wannan zanga-zanga saboda halin rashin tsaro da ƙasar ta tsinci kanta a ciki sanadiyyar hare-haren da ake kaiwa na bama-bamai da bindigogi musamman a yankin Arewa maso gabashin Najeriyar.
Yanzu haka dai ala tilas an kafa dokar hana fita na tsawon awanni 24 a wasu jihohin ƙasar don magance tashe-tashen hankula da ake dangantawa da zanga-zangar lamarin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bani Adama suke cewa na fakewa da guzuma a harbi karsana ne.
Mawallafi: Mohammed Al'amin Suleiman
Edita: Mohammad Nasiru Awal