1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Gambiya ya yi ta'adi a zamaninsa

Wally Omar RGB
December 6, 2019

Wani kwamitin sasantawa a Gambiya wato TRRC, ya kammala zaman jin koken jama'a kan laifukan keta hakkokin dan Adam da ake zargin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh da mukarabansa da aikatawa.

https://p.dw.com/p/3UMFC
Tsohon shugaban Gambiya  Yahya Jammeh
Tsohon shugaban Gambiya Yahya JammehHoto: picture-alliance/dpa/Taiwan Press Office

Kwamitin fadar gaskiya da sasantawa na Gambiya wato TRRC, ya saurari koken jama'a a game da laifuka na kisa da cin zarafi da gallaza wa jama'a ukuba ya zuwa fyade da tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh da mukarabansa suka aikata. Lauifukan an aikatasu a tsawon shekaru ashirin da biyu da shugaban ya kwashe yana mulkin kasar. Baba Hydara da ne ga dan jarida Dayda Hyadar da ake zargin jami'an tsaron Jammeh da hannu a kisansa, ya yaba da aikin kwamitin na fito da gaskiyar kisan mahaifinsa duk da dogon lokacin da aka kwashe....Ya ce: ''Kwamitin TRRC, ya bankado duk laifukan da aka aikata da kuma yi kokarin dannewa, amma yanzu sai ga wadanda suka aikata laifin da kansu sun amince da gaskiya, wannan ya kara fitowa karara da irin ta'asar da aka tafka na fyade da kisa na ba gaira ba dalili da laifuka na keta hakkokin bil' Adama, karon farko kenan da ake bankado gaskiya kamar haka a Gambiya'':

Sabbin shugabannin Gambiya na neman hukunta masu laifi a tsofuwar gwamnatin Jammeh

Sai dai da aka kwashi tsawon shekaru 17 kafin gaskiya ta yi halinta a kisan dan jaridan da ya janyo zazzafan martani daga sassan duniya a wancan lokacin. duk da haka dan marigayin ya baiyana shakku kan sakin wasu daga cikin mukaraban Jammeh da ake zargi da aikata laifukan duk da cewar sun amince da laifin bai dace a ce an sakesu ba inji Baba.

Shugaban Gambiya t Adama Barrow
Shugaban Gambiya Adama Barrow Hoto: picture alliance/abaca/X.Olleros

Ya ce: ''Sakin mukaraban na Jammehn ba tare da an fara tuntubarmu da sauran iyalan da lamarin ya shafa ba kuskure ne, mun nemi babban alkalin kasar Abubcarr Tambadou ya sauraremu amma ya ki, fatan da muke a  gurfanar da Jammeh gaban kotu.

Kwamitin na ci gaba da aikinsa duk da cewa ya tafi hutu inda ake fatan zai koma bakin aiki a shekara mai kamawa kafin a dora daga inda aka tsaya, batun da za a fi mayar da hankali zai kasance shirin da tsohon shugaban kasar na Gambiya Yahya Jammeh ya samar na kirkirar maganin warkara da cutar HIV Aids.