Yadda zaben raba gardama ya guda a Kirimiya
March 16, 2014Da misalin karfe bakwai na agogon Najeriya da Nijar ne 'yan Kirimiya suka fara dogayen layuka a gaban runfunan zabe na Simferopol da ke zama babban birnin yankinsu domin kada kuri'unsu. Hasali ma dai galibin wadanda aka tattauna da su sun bayana cewa sun amince da hadewar yankinsu da Rasha, saboda da ma wannan kasa da kuma Kirimiya tamkar dai Danjuma ne da Dan Jummai, ma'ana 'yan uwan juna ne baya ga dangantaka ta tarihi.
Ko da shi ke dai galibin 'yayan wannan yanki na da wannan ra'ayi, amma kumma ana ganin cewa dalilai na tattalin arziki ya sa su karkata zuwa ga kasar Rasha. Yankin na Kirimiya dai zai samu kulawa ta musamman ma daga hukumomin Moscow idan ya balle. Lamarin da zai bai wa tattalin arzikin tsibirin damar murmurewa, yayin da al'umma kuma za su samu karin ayyukan yi da kuma albashi mai tsoka.
Kerry ya ce zaben Kirimiya haramtaccen ne
Sai dai kuma a lokacin da suka tattauna da wayar tarho da abokin aikinsa na Amirka John Kerry, ministan harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov ya jadadda masa cewar zaben raba gardama na tsibirin Kirimiya na kan turba saboda ya dace da dokokin kasa da kasa. Amma kuma a nasa bangaren Kerry ya ce Kasashen Turai da kuma Amirka na daukan wannan zabe a matsayin haramtacce.
"Da ni da ministan harkokin waje Lavrov mun yi tattaunawa mai armashi. Sai dai bayan tattaunawar Lavrov ya nuna a filin cewa shugaba Putin ba zai ce komai ba har sai bayan kuri'ar raba gardamar. Sai dai kamar yadda muka sha fadi wannan zaben ya saba da kundin tsarin mulkin Ukraine, ya saba da dokokin kasa da kasa saboda haka haramtacce ne."
Kabilar Tatar na tsoron bayan zabe
Kamar yadda suka alkawarta tun da farko, kabilar Tatar wadanda galibinsu musulmi 'yan Sunnu ne sun kaurace wa zaben raba gardama na Kirimiya, duk kuma da alkawarin da aka yi musu na inganta halin rayuwarsu. Su dai Tatars wadanda kashi 12 daga cikin 100 ne na al'ummar Kirimiya sun kasance 'yan baya ga dangi saboda zarginsu da ake yi da taimaka wa 'yan nazi lokacin yakin duniya na biyu. Saboda haka ne kama daga wadanda suke da zama a Kirimiya har ya zuwa wadanda ke cin rani a ketare suke nuna fargaba game da makomar kabilarsu. ko da shi ma Olaf Leidreiter wani Tatar da ke da zama a birnin Bonn sai da ya nuna fargaba a kan komawa karkashin kasar Rasha.
"Muna tsoron ka da abin da ya faru a baya ya sake faruwa inda aka wulakanta 'yan Tatar na Kirimiya dubu 150 tare da kafa musu karar tsana bayan yakin duniya na biyu. Tarihi zai iya sake maimata kansa idan Kirimiya ta hade da Rasha. Saboda hake ne muke jin tsoro muke kuma nuna fargaba."
Babu dai wasu 'yan kallo daga manyan kasashe ko kuma kungiyoyi na duniya da suka shaidar da zaben na raba gardama. Sai dai kuma tun a ranar asabar, Rasha ta hau kan kujerar na ki lokacin da mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya suka yi yunkurin albarkantar kudirin da ke nuna cewa zaben ma Kirimiya haramtacce ne.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Suleiman Babayo