1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus na ma duniya barazana.

Binta Aliyu Zurmi
February 11, 2020

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce cutar Coronavirus na zama babbar barazana ga duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/3XbSt
Schweiz Genf | Pressekonferenz  WHO - Tedros Adhanom Ghebreyesus Ruft Gesundheitsnotstand wegen Coronavirus  aus
Hoto: picture-alliance/KEYSTONE/J.-C. Bott

A yayin kadamar da taron kwana biyu na kimiya a birnin Geneva na kasar Switzerland da zumar kara kaimi wajen samar da maganin  cutar.

Shugaban hukumar lafiyar, ya kara da cewar akwai bukatar kara bincike idan a ka yi la'akari da yadda cutar da ke yaduwa daga mutum zuwa mutum aka sameta a kasar Birtaniya da Faransa wanda babu wanda ya dauko cutar daga china ko ma wani dan Chaina da ya shiga kasashen biyu.

Ya zuwa yanzu dai cutar na ci da yaduwa wanda adaddin masu dauke da ita ke kara karuwa yayin da alluma da yawa ne suka mutu sanadiyar cutar a kasar Chaina.