Wata kotun kasar Masar ta ba da umarnin sakin Mubarak
August 21, 2013Wata majiyar shari'a da kuma ta jami'an tsaro a kasar Masar sun ce a wannan Laraba wata kotun kasar ta ba da umarni da a sako tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak. Abin nufi yana iya barin gidan kurkuku a ranar Alhamis kamar yadda lauyansa ya nunar inda ya kara da cewa babu wasu dalilai na ci gaba da tsare shi. Mubarak mai shekaru 85 an sake zaman sauraron shari'arsa a kan zargin ba da umarnin kashe masu zanga-zanga lokacin juyin juya halin shekarar 2011 wadda ta kai ga faduwar gwamnatinsa. Sai dai tuni ya kammala zaman wakafi na farkon shari'a kamar yadda aka amince dangane da wannan batu. A bara aka yanke wa Mubarak hukuncin daurin rai da rai don ya gaza hana kisan masu zanga-zanga. Amma a farkon wannan shekara wata kotu ta amince da karar da ya daukaka inda ta ba da umarnin sake sauraron shari'ar. A wani labarin kuma kungiyar EU na duba batun dakatar da hadin kai da Masar. A wannan Laraba ministocin harkokin wajen EU ke tattaunawa a birnin Brussels game da halin da ake ciki a kasar ta Masar.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu