1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu ba su ji dadin hukunta sojojin Nijar ba

Abdoulaye Mamane Amadou
January 29, 2018

A Jamhuriyar Nijar wasu Iyaye da dangin sojojin kasar da aka yanke wa hukuncin zama gidan yari bisa zargin yunkurin juyin mulki, sun bayyana ra'ayinsu game da yanda hukuncin ya gudana.

https://p.dw.com/p/2riDG
Niger Niamey Gefängnis Revolte
Wasu sojojin Nijar na tabbatar da tsaroHoto: STR/AFP/Getty Images

Kotun dai ta daure wadanda ta zarga ne daga shekaru biyar zuwa goma sha biyar a gidan yari, bayan da ta tabbatar da kama su da laifin. Lauyoyinsu sun ce za su tuntubi juna don sanin hanyar bi a yayin da ‘yan uwan jojojin ke nuna juyayi kan matakin kotun. Da yammacin ranar Asabar ne sakamakon karshe na zaman kotun da ke hukunta laifukan na soja ya bayyana wanda ya kai ga daure akalla mutum 9 daga cikin 12 da kotun ta tuhuma da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a cikin watan Disambar shekarar 2015.

Wasu sojojin Nijar na tabbatar da tsaro
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Daga cikin wadanda kotun ta yi wa hukunci mafi tsanani na daurin shekaru 15 a gidan yarin har da Janar Salou Soulaiman da ake zargin shi ne kanwa uwar gami wajen kitsa juyin mulkin, da kanal Issa Amadou Kountche da kuma Laftanal kanal Usman Awwal Hambaly da kotun ta tuhuma da wanda ya yi ruwa da tsaki inda kotun ta daure shi a tsawon shekaru 15. Sai dai Laftanal kanal Awal Hambaly wanda shi ma hafsan soja ne da ke a matsayin Uba ga Usman Awal Hambaly, ya nuna matukar damuwa game da sakamakon kotun.

Ya ce ‘‘wannan hukuncin ba dai dai ba ne, saboda sau uku kenan ake kama shi a ce wai yana son yin juyin mulki, ranar da aka kama shi na kai wata guda ina yawon neman sanin inda ya ke don kai masu abinci ban samu ba, kuma ni bance komai ba. Kamu  na uku kenan kuma ina ganin wannan ba dai dai ba ne‘‘

Niger Trauerfeier Beerdigung
Dandazon wasu daga cikin iyalan sojojin NijarHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Ko baya ga wadanda aka yanke wa hukuncin shekaru 15, zaman kotun ya kuma daure Hassan Shekaraou da Issoufou Oumarou da Amadou Salifou Sidi, a wa’adin shekaru 10 kowannensu, ko da yake tun daga farko babban mai shigar da kara ya bukaci kotun da ta daure wasunsu har na tsawon shekaru 20. To amma sai dai ‘yan uwa da aminan arziki, sun ce hukuncin ya zo masu a karkace.

Duk da hakan dai kotun ta daure Niandou Salou Souleymane da Janar Salou Soulaimen da Soumaila Amadou da Mahamadou Idrissa a matsayin wadanda za su yi shekaru biyar a gidan yarin. Doka dai ta tanadi damar zuwa kotun kare kukanka don duba dacewar hukuncin bisa tanadin dokokin kasa ko kuma akasin hakan.