Wasannin Bundesliga na bana sun zo da mamaki
A wasannin bana, kungiyar Bayern Munich ta tsaya kan kaifinta, yayin da RB Leipzig ta yi zarra a wasannin. Shi kuma Nils Petersen ya daga sunan kungiyar Freiburg.
RB Leipzig 3-1 Augsburg
Kungiyar Red Bulls Leipzig ta yi fice a wasannin hunturun bana, bayan lallasa Augsburg bayan zaburowar da ta yi lokacin da aka dawo hutun rabin lokaci. Da farko Florian Niederlechner na Augsburg ne ya nuna bajintarsa bayan Marco Richter ya shirya masa kwallon da ta burge 'yan kallo. Amma bayan rabin lokacin, kwallayen Konrad Laimer da Patrik Schick da ma Yussuf Poulsen suka farke wa kungiyar laya.
Cologne 1-0 Werder Bremen
Bayan gaza katabus a farkon kakar bana, sai ga kungiyar Cologne ta zama cikin na gaba-gaba. Jhon Córdoba ne tare da taimakon dan wasan tsakiya Markus Gisdol's, suka daga likafar kungiyar. Nasarar ke nan da ta samu a karawa 14 da ta yi. Haka ma ta kasance wa kungiyar Bremen, wadda ta sami nasara daya a karawa 13. Coach Florian Kohfeldt, na fuskantar matsin lamba.
Bayern Munich 2-0 Wolfsburg
Sau biyu cikin mako guda, Joshua Zirkzee, ya sama wa kungiyarsa ta Bayern maki uku. Dan wasan na Holland, ya danna ta ne daga bugun kusurwa ana minti 85 da fara wasa. Haka shi ma Serge Gnabry ya kara mintuna hudu bayan nan. Kafin shigar Zirkzee dai, ana iya cewa tafiyar Bayern ba ta yi ba, a lokacin ne kuma Wolfsburg ke ganin ita ce za ta kai labari.
Schalke 2-2 Freiburg
Canjaras aka tashi a birnin Gelsenkirchen a karawar da ta hada Schalke 04 da Freiburg. Schalke da aka buga a gidanta ce ta fara zura kwallo daga dan wasanta Suat Serdar, minti 26 da fara wasan. Sai dai fenariti da Nils Petersen dan Freiburg ya buga ya farke. Bayan rabin lokaci, Vincenzo Grifo na Freiburg ya sake zura wa Schalke, kafin daga karshe Ahmed Kutucu ya rama wa Schalke, minti 10 a tashi.
Hertha Berlin 0 - 0 Borussia Mönchengladbach
Da farko an yi zaton sabon kocin kungiyar Hertha Berlin Jürgen Klinsmann zai shigo da kafar dama, amma sai ga shi karawa uku babu ci. Da Berlin din da Borussia Mönchengladbach sun tashi ba kare bin damo. Dukkanin su dai sun taka leda gwargwado, sai rashin masu ci. Wannan dai koma baya ce ga koci Marco Rose na Mönchengladbach gabanin hutun kakar, ta la'akari da maki da kungiyar Leipzig ke da shi.
Mainz 0-1 Bayer Leverkusen
Kwallon da Lucas Alario ya zura bayan karin lokaci, shi ne ya taimaka wa kungiyar Leverkusen a karawarta da kungiyar Mainz. Shi dai Alario dan wasan gaba na Argentina, ya zura ta ne mintuna 10 da sa shi wasan, lokacin kuma da Leverkusen din ke da 'yan wasa 10. Hakan dai ga alama zai sanya farin ciki ga koci Peter Bosz a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara.
Hoffenheim 2-1 Borussia Dortmund
Kwallaye biyu ana gab da tashi da Sargis Adamyan da kuma Andrej Kramaric suka zura wa Borussia Dortmund, sun sanya murna ta koma cikin mai horas da 'yan wasan Dortmund, Lucien Favre. Mario Götze ne da fari ya ci wa kungiyar Borussia Dortmund kwallonta mintuna 17 da farawa, sai ga shi a karshe sun koma taɓa-ni-luɓus a karshen kakar.