1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Leverkusen ta rasa matsayinta a saman teburin Bundesliga

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
December 21, 2020

Kamaru ta samu tikitin shiga gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2021 na ‘yan kasa da shekaru 20 da haihuwa, a fagen boxing, Junior Makabu na Kwango ya doke dan Najeriya Olanrewaju Durodola.

https://p.dw.com/p/3n1BU
Deutschland Bundesliga Bayer 04 Leverkusen gegen FC Bayern München | Tor Lewandowski
Hoto: Inderlied/Kirchner-Media/imago images

Kamaru ta samu tikitin shiga gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2021 na ‘yan kasa da shekaru 20 da haihuwa, bayan da ta zo na biyu a wasannin tankade da rairaya na rukunin tsakiyar Afirka da aka kammala a ranar Asabar a birnin Malabo na Equatorial Guinea. Wannan damar ta samu ne bayan da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta doke takwarta ta Kwango Brazaville da 2-1, lamarin da ya mayar mata da hannun agogo baya, saboda Kwango Dimukaradiyya na bukatar doke ta Brazaville da 3-1 kafin ta kai labari. Alhahi a nata bangaren Kamaru ta yi nasarar lallasa Kwango Brazaville da 3-1 bayan da ta yi tashi ci daya ko ta ina a wasan da ta yi da Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango. Wannan ne ya sa Kamaru ta bi sahun Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wacce nasarar da ta yi a kan Equatorial Guinea (2-1) ya sa ta kammala wasan a saman rukuninsu.

Ita Kamaru wacce ta lashe kofin 'yan kasa da shekaru 20 a 1995, ta zama kasa ta 10 da ta cancanci shiga gasar ta Afirka baya ga Mauriteniya mai masaukin baki da Gambiya da Yuganda da Tanzaniya da Namibiya da Mozambik, sai Ghana da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Matsalar wariyar launin fata a kwallon kafar Brazil

Wani sabon rikici kan wariyar launin fata ya barke a Brazil kwanaki kalilan bayan na nahiyar Turai wanda ya shiga kanun labarun duniya. Dan wasan tsakiya na kungiyar Flamengo na Brazil Gerson ya zargi dan wasan tsakiyar Bahia dan kasar Colombia Juan Pablo Ramirez da furta kalaman nuna wariyar launin fata a kansa a ranar Lahadi a lokacin wasanbabban lig din kasar tsakanin bangarorin biyu. Tuni dai Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil (CBF) ta nemi Babbar Kotun Wasanni ta kasar da ta "hanzarta” gudanar da bincike a kan zargin wariyar launin fata don gaskiya ta yi halin ta.

Gerson na kungiyar Flamengo a wata karawa da Athletico Paranaense a Brazil
Gerson na kungiyar Flamengo a wata karawa da Athletico Paranaense a BrazilHoto: Reuuters/R. Buhrer

Gerson ya ce Juan Pablo Ramirez ya ce da shi "Yi min shiru, Bakar fata" lokacin da ya yi kokarin kwantar da rigimar da ta taso tsakanin dan wasan tsakiyar Bahia da takwaransa Bruno Henrique a minti na 52 da fara wasa, wanda Flamengo da lashe da 4 ta ci. -3. Mafi yawancin kulob kwallon kafa a  Brazil sun nuna goyon baya ga dan wasan tare da yin Allah wadai da wariyar launin fata. A Brazil da ta zama kasa ta karshe a yankin Latin Amirka da ta daina bautar da mutane, doka ta tanadi hukuncin daurin shekara daya zuwa uku a gidan yari a kan duk wanda aka samu da laifin nuna wariyar launin fata.

Leverkusen ta rasa matsayinta a saman teburin Bundesliga

Kungiyar Bayer Leverkusen ta rasa matsayinta na daya a teburin Bungesliga ta Jamus bayan da Yaya Baba Bayern Munich ta bi ta har gida ta doketa da 2-1 a filin wasa na BayArena a mako na 13. Wannan koma-bayan dai na matikar ci wa Leverkusen tuwo a kwarya kasancewar dan wasanta Patrich Schik ne ya fara zira wa abokan hamayya kwallo a raga kafin dodon raga na Munich wato Robert Lewandownski ya farke kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan ya maimata ana daf da busan karshe, lamarin da ya bakanta ran Peter Boss mai horas da Leverkusen.

A yanzu Bayern Munich ne ke saman teburi da maki 30 yayin da Leverkusen ke biyan mata baya da maki 28. Ita kuwa RB Leipzig tana ci gaba da zama a matsayi na uku da maki 28 saboda ba ta taka rawar gani a wasan da ta yi da Kolon nema da nema. Yayin da Dortmund ke ci gaba yin abin fallasa inda a wannan karon kuma Union Berlin ta lallasata da 2-1. A yanzu dai Dortmund na a matsayi na biyar, lamarin da ke dagula mata lissafi a kokarinta na zama zakara.

Ita ma Borussia Mönchengladbach ta baras da wasanta da ci 1-2 a gaban Hoffenheim, amma rashin da'a da dan wasanta Marcus Thuram ya nuna, inda ya tofa wa wani dan wasa miyau ne ya shiga kanun labarai.

Damben boxing a Afirka na WBC

A fagen boxing, dan damben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Junior Makabu ya doke dan Najeriya Olanrewaju Durodola a birnin Kinshasa a ranar Asabar, a kokarin kare kambunsa na WBC na ajin masu matsakaicin nauyi na duniya. Dan damben na Kwango ya yi wa takwarnsa na Najeriya kisan faraf daya a turmi na bakwai, duk da cewa Olanrewaju mai shekaru 40 ba kwawar lasa ba ne saboda ya lashe dambe 34 daga cikin 42 da ya fafatawa bayan da rungumi boxing a matsayin sana'a.

Südafrika Boxgirl-Schule
Hoto: DW/J. Jaki

A fannin kwallon hannu kuwa, Norway ta lashe  kwallon hannu na mata na nahiyar Turai da ci 22 da 20 a gaban Faransa. gasar wasanni da ke zama ta farko ta kasa da kasa a cikin annobar Covid-19, an buga daga 3 zuwa 20 ga Disamba a Herning na kasar Denmark. Rabon 'yan matan Norway su lashe gasar ta hannu tun shekaru hudun da suka gabata.