1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Finidi George ya yi murabus

Mouhamadou Awal Balarabe
June 17, 2024

Finidi Geoge da ke horas da Super Eagles ya ajiye aikinsa bayan da kungiyar kwallon kafar Najeriya ta ci gaba da samun komabaya.

https://p.dw.com/p/4h9zS
Finidi George
Finidi GeorgeHoto: Nigerian National Football Federation

Bayan rashin tabuka abin kirki cikin wasanni biyu na neman gurbi a gasar cin kofin duniya da ya yi a matsayin mai horas da Super Eagles Finidi George ya yi murabus daga matsayinsa. Dama dai hukumar kwallon kafa ta NFF da ma'aikatar wasanni ta Najeriya sun samu sabnin ra'ayin kan irin kocin da ya kamata a dauka don ceto Super Eagles daga mummunan matsayi da ta samu kan ta a ciki. A daidai lokacin da NFF ke neman a samo kwawarren koci daga waje domin samun biyan bukata, ita kuwa gwamnati ta nace kan mai horaswa na cikin gida a sakamakon rashin masu gida rana.

Jamus ta fara Euro 2024 da kafar dama

Kasashen Turai na ci gaba da kalubalntar junansu da nufin neman lashe gasar kwallon kafa ta wannan nahiya a karo na 17 da ke gudana a Jamus. Dukkanin tawagogin da ake kyautata musu zato sun yi nasara a wasan farko na rukuni, inda Jamus mai masaukin baki ta mamaye Scotland da ci 5-1 a yayin yaye kallabin Euro 2024. Ita kuwa Switzerland ta lallasa Hongari da ci 3-1, yayin da Spaniya ta samu nasara a kan Coartia da 3-0 a rukuni na biyu. A fafatawar da da ta yi, Italiya da ke rike da kofin kwallon kafa na Turai ta nuna wa Albaniya cewar ruwa ba sa'an kwando ba ne da ci 2-1.

 Ita kuwa Ingila da ba ta taba lashe kofin kwallon kafa na Turai a tarihinta ba, ta doke Sabiya da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Veltins-Arena da ke Gelsenkirchen. Godiya ta tabbata ga dan wasan tsakiya na Real Madrid Jude Bellingham da ya share wa Ingila hawaye ta zura kwallo tun a minti na 13 da fara wasa. Ko da kocin Three Lions wato Gareth Southgate sai da ya yi kira ga 'yan wasan Ingila da su kara kaimi a wasanni masu zuwa idan suna son hayewa mataki na gaba:

Gasar cin kofin Turai Euro2024
Gasar cin kofin Turai Euro2024Hoto: Antonio Calanni/AP/picture alliance

"Kungiyarmu ba ta da kuzari kuma hakan bai bani mamaki ba. Mun yi wasa mai kyau kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma za mu yi tasiri nan gaba idan muka ci gaba da wasa tukuru a tswon mintuna 90 da 'yan wasan suke da shi, wanda hakan zai taimaka mana wajen ci gaba."

A yanzu dai Ingila ce ke matsayi na daya a rukunin C, yayin da Denmark da Sloveniya ke biya mata bya da maki daya, ita kuwa Sabiya ta kasance 'yar baya ga dangi ba tare da maki ko da daya ba.

Kunnen doki daya tilo a wasannin farko

Sai dai daya-dayan wasa da aka yi kunnen doki shi ne wanda ya wakana tsakanin Sloveniya da Denmark inda aka tashi 1-1. Dan wasan Denmark Christian Eriksen ne ya fara cin kwallo a minta na 17  a daidai lokcin da ya cika kwanaki 1100 bayan matsalar bugun zuciya da ya samu a lokacin gasar Euro 2020, amma dai Sloveniysa ta rama wa kura aniyarta tare ma da samun nasara dag bisani. Sai dai bai hana Christian Eriksen nuna doki game da kwallon da ya zura ba:

"Na yi matukar farin ciki da taimaka wa kungiyarmu da wannan kwallon farko da na ci. Amma a bayyane yake cewar labarin zai bambanta da mun sami maki uku, lamarin da zai sanya mana farin ciki tare da kara mana kwarfin gwiwa kafin mu shiga wasa na gaba."

Lewandowski dan wasan kasar Poland
Hoto: Johann Groder/Eibner Europa/IMAGO

A nata bangaren, Poland ta zakakurin dan kwallo Lewandowski ta sha kashi a hannun Netherlands ko Holland a filin wasa na Volksparkstadion da ke Hamburg da ci 1-2. Dan wasan gaba na Poland Adam Buksa ne ya fara cin kwallo a minti na 16 da fara wasa, kafin daga bisani reshe ya juye da mujiya inda Gakpo na Holland ya farke kwalle yayin da Wegourts ya sa bakin alkalami ya bushe a karshen wasa.

Amma kafin a fara wannanin na neman lashe kofin Euro 2024, hukumomin Jamus sun yi bikin budewa mai kayatarwa, inda aka yi kade-kade da raye-raye na tsawon mintuna 20 kafin Heidi Beckenbauer, matar dan wasan kwallon kafa kuma koci Franz Beckenbauer ta kawo kofin gasar Euro a wajen bikin. Ta samu rakiyar fitattun 'yan wasan kwallon kafar Jamus guda biyu, Jürgen Klinsmann da Bernard Dietz. Saboda haka ne Julian Nagelsmann, kocin Jamus ya samu kwanciyar hankali bayan da Manschaft ta samu nasara a kan Scotland ya wasanta na farko.

Euro2024: Magoya bayan Slovenia da Denmark
Hoto: Markus Ulmer/Pressebildagentur ULMER/picture alliance

"Yana da mahimmanci a gare mu mu samu nasara a matakin farko, shi ne tubalin da za mu iya dora gininmu a aki. Za mu yi kokarin mu kai labari a ranar Laraba. Ina da yakinin iya yin nasara a wannan wasa da Hungary a Stuttgart. Yanzu muna shiryawa sosai. "

A yanzu dan wasan tsakiya na Jamus Toni Kroos ya kasance a kan gaba na wadanda suka fi yanke abokan karawa wajen mika kwallon, inda mujallar wasanni ta "Opta" ta ce ya yi nasarar yanke 'yan wasa a 99% a yunkurin da ya yi, lamarin da ba a taba ganin irinsa ba tun 1980.

kasuwar musayar 'yan kwallo ta kankama a Turai

Manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai na ci gaba da hada-hada a kasuwar musayar 'yan wasa na lokacin bazara. A Faransa dai, kungiyoyin na taka tsantsan wajen sayen sabbin 'yan wasa saboda matsalar kudi da za su iya dogara da su  da rashin sanin adadin hakkokin talabijin na kakar wasa mai zuwa ba.  Amma a Jamus,  Bayern Munich ta nuna sha'awar sayan dan wasan tsakiya na Cystal Palace Michael Olise, inda ta kai ga tuntubar kungiyar da dan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara 22 ke buga wa. Shi kuwa Mats Hummels da ke a karshen kwantiraginsa da Borussia Dortmund ya fara tattaunaw da AS Roma ta Italiya.

EURO2024: Karawar Sabiya da Ingila
Hoto: Alexandra Fechete/imago images

A ingila kuwa, Newcastle na son dan wasan Chelsea Noni Madueke, yayin da Manchester United ke son dan wasan Bayern Munich haifaffen Holland Matthijs de Ligt. A bangarensu, Liverpool da Manchester United na son  dan wasan baya na Faransa Leny Yoro, a daidai lokacin da ita ma kungiyar Real Madrid ta nunar sha'awar sayan wannan dan wasan. Hakazalika, da wasan Roma Tammy Abraham na samun tayin daga Kungiyoyi uku wato Tottenhamda Aston Villa da West Ham

DeChambeau ya zama gwarzo a fannin golf

Dan Amirka Bryson DeChambeau ya lashe babbar gasar golf ta US Open da aka kammala a karshen mako a jihar North Carolina ta Amurka, a gaban dan kasar Ireland ta Arewa Rory McIlroy da ya taba lashe gasar sau hudu.  Wannan dai shi ne karo na biyu da DeChambeau mai shekaru 30 ya lashe wannan kambu, baya ga wanda ya taba lashewa a shekarar 2020.  McIlroy mai shekaru 35 ya kasance a sahu na biyu na gasa ta Golf, yayin da 'yan Amurka biyu Tony Finau da Patrick Cantlay suke tafiya kafada d kafada a matsayi na uku. Sai dai dan wasan Amurka mai lamba 1 Scottie Scheffler da aka yi waje road da shi tun a zgayen farko ya koma matsayi na 41 a gasar.