1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundesliga a Jamus da gudun fanfalake na farko a Kaduna

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
November 23, 2020

Gasar gudun fanfalake a karon farko a Kaduna da ke Najeriya da nufin bunkasa harkokin wasanni da karfafa zaman lafiya da hadin kai a kasar.

https://p.dw.com/p/3limK
Fußball Bundesliga | Bayern München - SV Werder Bremen
Hoto: Matthias Schrader/AP Photo/picture alliance

Dubban 'yan wasan tsere sun gudanar da gasar gudun fanfalake a karon farko a jihar Kaduna da ke Najeriya da aka yi wa lakabi da First-Kaduna–Marathan-runing-race, da nufin bunkasa harkokin wasanni da karfafa zaman lafiya da hadin kai a kasar. Za mu leka wasannin lig-lig na nahiyar Turai domin jin wainar da aka toya.

Bari mu fara Labarin Wasannin daga gasar Bundesligar kasar Jamus, inda wasan da Borussia Dortmund ta buga da Hertha Berlin ya zamo guda daga cikin wanda ya fi daukar hankali, a mako na takwas na kakar wasannin na bana. Ba wai kawai kwallaye biyar da Dortmund din ta samu nasarar zurawa a raga ne ya sanya wasan ya fi daukar hankali ba, sai dai yadda Youssoufa Moukoko ya kafa tarihi a matsayin dan wasa mafi karancin shekaru da ya buga a kakar wasannin Bundesliga ta Jamus din.

Dan wasa mafi karancin shekaru a Bundesliga

Moukoko haifaffen kasar Kamaru, ya bugawa kungiyarsa ta Borussia Dortmund yana da shekaru 16 da kwana daya a duniya, bayan da ya canji dodon ragar Dortmund din wato Erling Haaland a mintuna na 85 da fafatawar da Dortmund ke yi da takwararta ta Hertha Berlin a can Berlin fadar gwamnatin kasar Jamus.

Youssoufa Moukoko a karawa tsakanin Hertha da Borussia Dortmund
Youssoufa Moukoko a karawa tsakanin Hertha da Borussia DortmundHoto: Annegret Hilse/REUTERS

Da shekaru 16 da kwana daya cal, ya rusa tarihin da takwaransa Nuri Sahin da shi ma ke bugawa Dortmund din. Sahin da ya fara buga kwallo a kungiyar Dortmund yana da shekaru 16 da watanni 11 a shekara ta 2005. Moukoko wanda mai horas da 'yan wasan na Dortmund, Lucien Favre ya nunar da cewa yana jin dadin horas da shi dai, ya canji Haaland ne bayan da dodon ragar na Dortmund ya zura kwallaye hudu a raga, cikin biyar din da Dortmund din ta zura a ragar Hertha Berlin, inda aka tashi wasan Dortmund na da kwallaye biyar yayin da mai masaukin baki Hertha Berlin ke da kwallaye biyu.

A sauran wasannin da aka fafata kuwa, a ranar Asabar Leverkusen ta bi Armenia har gida ta kuma lalasata da ci biyu da daya, Mönchengladback da Augsburg sun tashi kunnen doki daya da daya yayin da aka tashi canjaras uku da uku tsakanin kungiyar Hoffenheim da Stuttgart. Shalke ta kwashi kashinta a hannu da ci biyu da nema a hannun Wolfsburg da ta kai mata ziyara, an kuma tashi kunnen doki daya da daya tsakanin Frankfurt da Leipzig kana ita ma Bayern Munich ta yi kunnen doki daya da daya da kungiyar Werder Bremen da ta yi tattaki zuwa birnin na Munich, kuma wannan wasanne ma sashen Hausa na DW ya kawo muku.

Premier League da La Liga

Karawa tsakanin Aston Villa da Liverpool cikin watan Oktoba
Karawa tsakanin Aston Villa da Liverpool cikin watan Oktoba Hoto: Catherine Ivill/Getty Images

A gasar Premier League ta kasar Ingila kuwa, a ranar Asabar Aston Villa ta sha kashi a hannun Brighton da ci biyu da daya, Tottenham ta lallasa Man City da ci biyu da nema Man United ta samu nasara a kan West Brom da ci daya mai ban haushi. A ranar Lahadi Everton ta bi Fulham har gida ta lallasa ta da ci uku da biyu, yayin da aka tashi canjaras babu ci tsakanin Leeds da Arsenal, Liverpool kuma ta yi wa Leicester cin kaca uku da nema. A La Ligar kasar Spain kuwa a ranar Asabar Villarreal da Real Madrid sun tashi kunne doki daya da dayainda Atletico ta lallasa Bercelona da ci daya mai ban haushi.

Gudun fanfalake don kyautata zaman lafiya a Najeriya

Yanzu kuma bari mu leka Tarayyar Najeriya, inda aka gudanar da gudun ya da kanin wani ko kuma gudun fanfalake karo na farko a jihar Kaduna, da nufin bunkasa harkokin wasanni da kuma karfafa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al'ummar kasar. Wakilinmu na Kadunan Ibrahima Yakubu na dga cikin wadanda suka kashe kwarkwatar idonsu a gasar da a cewarsa ta yi armashi sosai, bisa daga dukkan alamu kalliya za ta mayar da kudin sabulu.