Wakoki kan fa'idar zaman lafiya a kudancin Kaduna
January 11, 2017Kashe-kashen da ke addabar mutanen kudancin Kaduna, sun sa yanzu haka wasu kungiyoyin mawaka shirya wakoki na kira ga matasa da sauran mazauna wannan yanki da su rungumi zaman lafiya da yin sulhu da juna.
Ire-iren wakokin dai na kira ne a kan fa'idar zaman lafiya da kawar da gaba tare da kuma tabbatar da ganin cewa kowane matashin yankin ya bada tasa gudunmawar a fafatukar da hukumomi da kungiyoyin wanzar da zaman lafiya ke yi don magance tashe-tashen hankula da ke ci-gaba da janyo rarrabuwar kawunan daukacin al'umman yankin.
Danzaki Jogai shi ne shugaban mawakan "911 Studio" da ke bayyana irin shirye-shiryen da suke yi musamman ma dai na hada kan matasa mawaka a kan yin wakokin janyo hankalin kudancin Kaduna a kan zaman lafiya dan ci-gaban al'umma.
"Ni da kaina ne na ga cewa lokaci ya yi na kirkiro wasu hanyoyi da dabaru a kan hada kan al'umma don kawo karshen zubar da jinin da ake yi a yankin. "Muna ganin cewa akwai bukatar ilmantar da mutane da sauran kabilu ta hanyar wakokinmu a kan muhinmancin zaman tare domin magance matsaloli da suka jibanci na rashin tsaro a sanadiyyar wadannan tashe-tashen hankula da suka dade suna janyo mana koma baya."
Ganin yadda matasa ke amfani da kafar sadarwa ta Internet, hakan ne sanya mawakan ke tura wakokinsu ta wannan kafa domin fargar da matasa a kan rungumar zaman lafiya tare kuma da tattaro mawakan kan zuwa kasuwannin karkara don fadakarwa kan zaman lafiya.
Gudunmawar da kungiyoyin addinai ke bayar
To dangane da wannan mataki na fadakar da al'umma a kan muhimancin zaman tare, tuni su ma kungiyoyin malaman addinai a kasar suka himmatu wajen bullo da wasu hanyoyin wayar da kan mabiya kan zaman tare inji sakataren kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN reshen jihar Kaduna Rev. Sunday Ibrahim.
"Daga cikin matakan da muke dauka, mun fara da kiran daukacin Kiristocin kasar a kan yin addu'ar zaman makoki, sannan kuma muna ci-gaba da wayar da kan mabiyanmu a wuraren ibadu a kan fa'idar zaman lafiya . Muna kuma ci-gaba da janyo hankalin gwamnati a kan girke isassun jami'an tsaro a yankin don magance ci-gaba tashe-tashen hankula nan da can."
Sheikh Usman Abubakar Babantune, shi ne shugaban kungiyar majalisar limamai da alarammomi a Kaduna da ke cewa:
"Zaman lafiya ne hanya daya tilo da ya kamata a bi domin magance wadannan rigingimu. Muna yin dukkanin kokarin da suka wajaba domin ganin an kawo karshen wadannan rigingimu. Idan babu zaman lafiya babu wani ci-gaban da za a iya samu, saboda haka lallai wajibi ne gwamnati ta taimaka wajen sauraran abunda za mu iya bata don kara daukar matakan dakile wadannan fitintinu."
Babban burin da mawakan shi ne na ganin matasan kudancin Kaduna su rika kauce wa yadda wasu 'yan siyasa ke amfani da su wajen cimma burinsu na daban.