1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Kenya da Jibuti

Antonio Cascais, ZMA/LMJ
June 17, 2020

Kasasahen Afirka kan yi magana da murya guda idan batun zabar wakilin nahiyar ya taso a wata hukumar duniya. Sai dai a yanzu wata takaddama na neman kunno kai tsakanin Kenya da Jibuti.

https://p.dw.com/p/3dvxE
Sicherheitsrat der UN berät Erhaltung des Weltfriedens
Takaddama kan kasar da za ta wakilci Afirka a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Hoto: picture-alliance/dpa/Xinhua

Daga bangaren Kenya dai, akwai alamun cewar kwalliya za ta biya kudin sabulu, domin a zaben sirrin da ya gudana a watan Fabarairu, kasashen Afirka da ke da wakilci a kungiyar Tarayyar Afirka sun zabe ta a matsayin wakiliyar nahiyar, a daya daga cikin zaunannun kujerun Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar da za a nemi cikewa daga watan Janairun 2021.

Kenya ko Jibuti? Wa zai gaji Afirka ta Kudu?

Da nasarar kuri'un amincewar kasashe 37 da adawar 13, Kenya ta zamo mai maye gurbin Afirka ta Kudu a karshen wa'adinta, saboda nasararta a kan Jibuti, sai dai kwatsam shalkwatar kungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa ta samu wasika daga Jibutin. Karamar kasar ta yankin Kahon Afirka da ke magana da harsunan Faransanci da Larabci, na neman kungiyar Tarayyar Afirka ta sake nazarin matsayinta.
A cewar jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniyar, goyon bayan da AU din ta nunawa Kenya ya saba ka'ida. Dr Roba Sharamo da ke zama daraktan cibiyar nazarin harkokin tsaro a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, ya ce wannan matsala ce ta banbancin yankunan. A lokacin zaben kasar da za ta wakilci Afirkan a watan Fabarairun dai, akwai fargabar cewar zabar Jibuti na nufin, nahiyar ta Afirka za ta samu wakilcin kasashen Afirka da ke magana da harshen Faransanci har uku a shekara ta 2021, saboda Nijar da Tunisiya za su maye gurbin sauran kujeru biyun na Afirka a Majalisar.

Ismail Omar Guelleh
Shugaban kasar Jibuti Ismail Omar GuellehHoto: picture-alliance/dpa

Rainon Faransa ko rainon Ingila?

A wasikarta zuwa ga AU, Jibutin ta yi watsi da wadannan batutuwan, a cewarta an yi hakan a baya a shekara ta 2000, lokacin da Mali da Moritaniya da Tunisiya suka wakilci Afirka a kwamitocin Majalisar Dinkin Duniyar a lokaci guda.

To sai dai masanin kimiyar siyasar Kenya Martin Oloo, ba ya ganin takaddamar a matsayin banbancin harsunan Faransanci ko Turanci a bangaren kasashen Afirkan kamar yadda ake hasashe, sai dai kawai za a iya cewa hakan na bayyana rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen yammaci da kuma na gabashi. A cewar masanin kimiyyar siyasar dai, akasarin kasashen Afirka da suka samu wakilci a kwamitin sulhun, ba su yi wani abu na azo a gani ba, na cimma muradun kasashen nahiyar. Duk da da cewar akwai tarin matsaloli da ke bukatar a shawo kansu cikin gaggawa a Majalisar, har yanzu ba a la'akari da muryar Afirkan.