1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Dangantaka da Afirka ta Yamma

Daniel Pelz AH/LMJ
August 26, 2021

Za a iya cewa, babu wani yanki a duniya da Merkel ta mayar da hankali a kansa tsawon mulkinta kamar yammacin Afirka. Kama daga jibge sojojin Jamus a Mali da batun bakin haure har zuwa batun tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3zTRu
Deutschland Berlin | Konferenz Compact with Africa | Angela Merkel, Bundeskanzlerin | Gruppenbild
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a taron kungiyar G20 da shugabannin AfirkaHoto: Reuters/F. Bensch

Yankin yammacin Afirka zai kasance abin kulawa da zai taka muhimmiyar rawa ko an samun sabuwar gwamnati a Jamus, bayan Angela Merkel ta kammala mulkinta. Babu dai wani daga cikin yankin da ya ja hankali gwamnatin Merkel kamar na yammacin Afirkan, kama daga batun sojojin Jamus a Mali da batun 'yan cirani da na tattalin arziki. Abin da ake kyautata zaton cewar zai ci gaba da dorewa a sabuwar gwamnatin da za ta zo. 

Karin Bayani: Taron saka jari tsakanin Jamus da Afirka

Rantsar da shi ke da wuya a matsayin sabon shugaban kasar Nijar cikin watan Yulin da ya gabata, Shugaba Mohammed Bazoum ya kai ziyara ta yin ban kwana ga shugabar gwamnatin Jamus din. Bazoum ya jinjinawa Jamus kan yadda take tallafawa Nijar da ma yankin yammacin Afirka da ya ce ta yi ruwa ta yi tsaki a cikin batun tsaro. Sai dai labari maras dadi na zuwa daga yankin na Sahel, inda kusan kowane mako ake kai hare-hare na ta'addanci ko dai a Burkina Faso ko kuma Nijar, baya ga fada tsakanin makiyaya da manoma a Mali.

Deutschland Berlin | Treffen Angela Merkel und Mohamed Bazou aus Niger
Ziyarar shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ga Angela MerkelHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Mutane kusan miliyan 30 a yankin ke bukatar agajin jin kai. Hakan dai ya sa hukumomi a birnin Berlin cikin fargaba a kan karuwar ayyukan 'yan tarzoma da ta iya janyo kwararrar 'yan cirani zuwa nahiyar Turai, idan yankin ya gaza wajen iya taka birki ga hare-haren. Da ma dai wasu kasashen Afirka ta yamma, sun kasance mashigi ko kuma hanyar shiga Turai daga wasu kasashen. Siyasar Jamus a yankin na yammacin Afirka ta kasu a kan manufofi uku , wato tsaro da raya kasashe da kuma yaki da kwararar 'yan cirani. Misali karara shi ne dakarun Jamus 1000 da ke cikin rundunar kungiyar Tarayyar Turai ta EUTM da ke kula da bayar da horo da kuma rundunar MINUSMA.

Karin Bayani: Kafa rundunar sintiri ta Turai a Sahel

Sai dai duk da yawan rundunonin har yanzu an gaza tsaida ayyukan ta'addanci a yankin na Sahel, a cewar Nadiya Adam ta wata cibiyar da ke gudanar da bincike a kan sha'anin tsaro a Malin cikin wata hira da aka yi da ita tun cikin watan Yuli. Jamus din za ta ci gaba da fuskantar matsin lamba, saboda shugaban Faransa Emmanuel Macron zai janye sojojinsa 2000 daga yankin nan da shekara ta 2022. Wata rundunar nahiyar Turai za ta maye gurbinsu, koda yake kawo yanzu Jamus ba ta cikin tsarin amma za a iya neman agajinta in abubuwa suka rinacabe.

Nigeria Besuch der Kanzlerin Merkel
Angela Merkel tare da shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/A. Akunleyan

Sabuwar gwamnatin da za ta zo, za ta ci gaba da aiwatar da shirin yaki da kwararar bakin haure. Najeriya da Ghana sun kasance masu yawan al'ummar da ke ficewa yayin da Nijar ke zaman hanya daga Agadez zuwa Libiya zuwa Turai. Jamus ta kan bayar da makudan kudi na bayar da horo ga 'yan sandan kan iyaka. Misali a Nijar, gwamnatin ta Jamus ta kaddamar da wani shiri na kare kan iyakoki da ya ci kudi miliyan shida na EURO. Koda yake Stephan Adaawen wani kwarare a kan batun yin kaura a Ghana ya ce shirin ya gaza. A fannin tattalin arziki kuwa, kamfanonin Jamus na yin dari-dari da yankin na yammacin Afirka wajen zuba jari. Ko da yake a baya-bayan nan kasar ta kadammar da wani shiri da aka yi wa lakabi da "Compact with Africa", wanda ya hada da kasashen yankin yammacin Afirka da yanzu za a iya damawa da su.