Wa zai gaji kujerar shugabar gwamnati Angela Merkel?
Har yanzu jam'iyyar hadakar Merkel ta CDU/CSU ba ta tsayar da mai maye gurbinta a zaben kasa na 2021 ba. Amma tuni SPD ta fitar da dan takararta. Kana jami'iyyar kare muhalli ta the Greens, na da 'yan takara biyu.
Armin Laschet
Shugaban jam'iyyar CDU Armin Laschet, jajirtaccen me goyon bayan Angela Merkel, kuma gwamnan jiha mafi yawan jama'a a Jamus. Me shekaru 59, ya kasance mai yawan barkwanci da kaunar hadin kai da sasantawa. Amma a baya-bayan nan wannan halayyar ta sha sa shi yin amai yana lashewa, lokacin ta'azzarar coronavirus.
Markus Söder
Me kaifin basira wajen hangen nesa: Gwamnan Jihar Bavaria mai shekaru 54 dan jam'iyyar CSU, ya samu goyon bayan al'umma dangane da irin jajircewarsa wajen yaki da annobar coronavirus. "Bavaria Jiha ce mai karfi. Bavaria za ta girma. Bavaria ta kafu. Bavaria na cikin kariya... kuma haka za ta ci-gaba da kasancewa,". Wadannan su ne kalaman tsohon dan jaridar a farkon mulkinsa a shekara ta 2018.
Olaf Scholz
Kara dusashewar tauraronta a kowane zabe, ya sa jam'iyyar SPD fitar da mai gaskiya maimakon mai tsattsauran ra'ayi a matsayi don takarar babbar kujerar a zaben 2021. Ministan kudi Olaf Scholz, tsohon magajin garin Hamburg, kana mataimakin Merkel a gwamnatin kawance, ana masa kallon dan jari hujja. Yawancin 'yan jam'iyyarsa sun ce mai shekaru 62 din, ba zai tabuka komai ba, balle ya samu karbuwa.
Jens Spahn
Ministan lafiya Jens Spahn, tauraro mai tashe na jam'iiyYar CDU, ya samu karbuwa daga al'umma lokacin annobar coronavirus, amma kuma ya samu suka. Dan shekaru 40 da haihuwa ya kasance dan luwadi da ke da aure, kana yana da kwarewa a harshen Turanci. Spahn ya hade da Armin Laschet a takarar shugabancin CDU, sai dai bai fito fili ya ayyana cewar ba shi da ra'ayin takarar shugaban gwamnati ba.
Robert Habeck
Me shekaru 51 Robert Habeck, ya kasance mai iya jawabi na jan hankali, ya na da basirar magana daidai da yanayin da ake ciki, ta hanyar yawancin Jamusawa 'yan siyasa ba su iya ba. Amma a wasu lokuta yakan kauce wa hanya a kan ainihin abun da ake magana a kai. Kafin ya shiga harkokin siyasa shekaru 20 da suka shige, ya kasance marubucin litattafai musamman na yara.
Annalena Baerbock
Da shekaru 41, Annalena Baerbock ta kasance daya daga cikin shugabannin jam'iyyar kare muhalli tun 2018. Masaniyar shari'a mai digiri a dokar kasa da kasa daga makarantar tattalin arziki ta London, magoya bayanta sun fi aminta da ita fiye da Habeck. Masu adawa da ita kuwa na sukar ta da rashin kwarewa a gudanarwar gwamnati da kuma salonta na amsa tambayoyin 'yan jarida.