Volkswagen - Kamfani a sassan duniya
Kamfanin Volkswagen VW na da masana'antu 119 a fadin duniya ya kuma dauki ma'aikata 600,000 a kasashen Turai 20 hadi da kasashe 11 na yankin Asiya da Amirka da Afirka. An kafa kamfanin VW karon farko a Wolfsburg a 1938.
A duk dakika ana siyar da VW a China
Kamfanin na VW ya kasance na farko daga kasashen Yamma da ya zuba jari a China lokacin da tattalin arzikinta ke bunkasa a tsakiyar shekarun 1980. A birnin da ke arewacin China na Changchun, VW ya yi hadin gwiwa da kamfanin China First Automotive. VW ya bude sabon kamfani a wannan birni a shekarar 2013.
Hoto bayan warware takaddama da ta gabata
"Kirar Jamus- da za ka aminta da mu," wannan dai shi ne tallan da aka rubuta a wannan mota ta VW kirar Passat a China. Zuba jarin VW a China labari ne me dadi. VW na da kamfanoni 13 a China hadi da sabon da aka bude a watan Mayu a birnin Changsha da ke kudanci.
A Indiya kananan motoci sun fi kasuwa
VW na da kamfanoni uku a Indiya. Kamfanin na "Volkswagen Group India" na aiki ne a birnin Pune inda yake da kamfani da ya dace da sabbin kamfanonin na VW da ke a sassan duniya. A shekarar 2010 an yi biki na kera samfirin Polo 11,111,111 wanda tsohon shugaban Jamus Horst Köhler ya halarta.
VW na da tarihi a Afirka ta Kudu
Volkswagen a Afirka ta Kudu na da sansani a birnin Uitenhage kusa da Port Elizabeth. Kamfanin ya fara aiki kusan shekaru 80. Ya fara aiki shekaru hudu bayan kafa kamfanin na VW a Jamus. Kimanin motoci 120,000 ake kerawa a Uitenhage duk shekara. A watan Agusta VW ya bayyana samar da gyara da fadada kamfaninsa. A Afirka ta Kudu VW na rige-rige da kamfanin Toyota wajen siyar da motoci a duniya.
Biyayya ga Rasha
Duk da tsamin dangantaka a matakin shugabannin siyasa, kamfanonin Jamus da dama ciki kuwa har da VW na biyayya ga Rasha. VW ya kasance babban me zuba jari a harkokin samar da motoci a Rasha. Firaminista Dmitri Medvedev ya halarci bikin kaddamar da sabon kamfanin kera injinan VW a Kaluga farkon watan Satimba, kamfanin da ke samar da injina 150,000 a duk shekara.
Babu ciniki sosai a Amirka
Lokacin da aka bude sabon kamfanin VW a Chattanooga, a jihar Tennessee a 2011, VW na da buri a kasuwar Amirka, amma cinikin ya yi kasa da yadda aka yi tsammani kamar yadda Ferdinand Piëch shugaban kamfanin ke fadi; "Mun fahinci kasuwar Turai, da China, amma mun gaza fahimtar Amirka" Wasu kwararru na ba da shawarar cewa VW ya fice daga Amirka tun bayan badakalar motoci masu amfani da man diesel.
Labarun nasara a Mexiko
VW na kera motoci a birnin Puebla a Mexiko kusan shekaru 60. Kamfanin Volkswagen de Mexico shi ya fi ba da aiki a wannan gari, yana da ma’aikata 15,000. Anan ana hada tsohuwar VW da ake kira Beetle har sai a 2003. A yanzu kamfanin da ke a Puebla na kera samfuran Passat da Jetta da sabuwar Beetle wacce ake fita da ita zuwa sama da kasashe 100.
¡Buen día Volkswagen!
Volkswagen na da wurin hada motoci bakwai a yankin Latin Amirka. An kafa hedikwatar VW Argentina a Cordoba, birni na biyu mafi girma a kasar. Anan kamfanin na da ma’aikata 1,500. A kan hada bangarori na motar VW anan, a kuma rarraba zuwa sassa daban-daban na duniya.
A Brazil an fi bukatar kananan motocin bas-bas
Brazil na da kamfanoni bakwai na VW ta kuma kasance kasa ta uku bayan Jamus da China inda aka fi hada motocin. An kafa kamfanin a birnin Sao Bernardo do Campo a shekarar 1953. Bayan lokaci kuma kamfanin Volkswagen do Brasil ya fara fitar da samfurin motocinsa, ciki har da irin wannan bas-bas da aka fi siya a kasuwannin kasashen Amirka ta Kudu da Afirka.