Putin ya soke wata ziyarar da ya shirya kai wa a Faransa
October 11, 2016Talla
Ziyarar ta Vladmir Putin wacce ba ta aiki ba ce, an dade da tsarata domin halartar wani bikin kaddamar da wata Cocin Orthodox ta Rashar a birnin Paris.Sai dai masu aiko da rahotannin sun ce shugaban na Faransa yana yin dari-darin ganawa da shugaban na Rasha a Fadar Elysée,sakamakon zargin da ake yi wa gwamnatin shugaba Bashar al Assad na Siriya da laifin aikata kisan kare dagin a Aleppo,tare da taimakon sojojin Rasha.Rikicin diflomasiya ya kara zafafa tsakanin kasashen yammacin duniya da Rasha,tun bayan da Rashar ta hau kujera naki a kan kudirin MDD wanda Faransa ta gabatar na tsagaita wuta a yakin da ake yi a Aleppo.